Shugaban Zambia ya ziyarci rumfar Sin a taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na ƙasarsa karo na 94

Daga CMG HAUSA

A jiya Lahadi ne shugaban ƙasar Zambia Hakainde Hichilema, ya halarci taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na ƙasar sa karo na 94, inda ya ziyarci rumfar ƙasar Sin, irinta ta farko da Sin ɗin ta kafa a baje kolin.

Taken baje kolin na bana shi ne “Fasaha ke ingiza ƙirƙire ƙirƙire-Fasaha ke sauya kasuwanci”.

A bana baje kolin na Zambia, ya samu tarin kamfanonin Sin mahalarta, cikin kamfanoni kusan 110, waɗanda suka shafi sassa daban daban, kamar fannin shuka tsirrai, da sarrafa na’urorin aikin gona, da na sarrafa albarkatun noma.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan