Sin: An samu ƙaruwar adadin cibiyoyin cajin ababen hawa masu amfani da lantarki

Daga CMG Hausa

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a shekarar bana, adadin cibiyoyin cajin ababen hawa masu amfani da lantarki na karuwa cikin sauri a sassan kasar Sin. Karuwar wuraren cajin na lantarki ko EVs, ya samar da dama ta biyan bukatun al’ummar kasar, wadanda ake amfani da nau’o’in ababen hawan dake amfani da lantarki.

Rahotanni daga hadakar kungiyoyin dake rajin bunkasa samar da na’urorin cajin ababen hawa masu aiki da lantarki ko EVCIPA, sun ce ya zuwa karshen watan Nuwamba, adadin irin wadannan cibiyoyin caji sun kai kusan miliyan 4.95, wanda hakan ke nuna karuwar kaso 107.5 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokacin na bara. Kaza lika tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bana, an kara kimanin irin wadannan wurare na caji har miliyan 2.33 a sassan kasar ta Sin.

Bisa jimilla, adadin wuraren cajin sun ninka wadanda ake da su a shekarar bara, kuma cibiyoyin cajin na sassa masu zaman kan su, su ma sun ninka har sau 4, cikin watanni 11 na farkon shekarar nan, idan an kwatanta da karuwar su a wasanni 11 na shekarar.

Ana alakanta wannan babban ci gaba da aka samu, da fadadar sashen amfani da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi na kasar Sin. Daga watan Janairu zuwa Nuwamba, adadin ababen hawa masu aiki da lantarki da aka saya a Sin, sun kai miliyan 6.07, adadin da ya ninka na sabbin cibiyoyin cajin da aka samar a tsakanin wa’adin har sau 2.6, wanda hakan ke nuni ga cewa, ana cimma bukatar saurin bunkasar sashen kamar yadda ake fata.

Mai fassara: Saminu Alhassan