Sin: Makullin warware rikicin Ukraine yana hannun Amurka da NATO

Daga CMG HAUSA

Dangane da zargin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi a baya-bayan nan cewa, wai ƙasar Sin ba ta yi Allah-wadai da matakin soja da Rasha ta ɗauka ba. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Zhao Lijian, ya bayyana Alhamis din nan cewa, kalaman da ɓangaren Amurka ya yi kan ƙasar Sin kazafi ne, kuma hakan ya ƙara fallasa ra’ayin ɓangaren Amurka na yakin cacar baka da yin fito na fito. Kuma irin waɗannan kalamai ba za su taimaka wajen magance matsalar ba, kuma Sin na adawa da su matuƙa.

Zhao Lijian ya ce, matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka kan fadada ƙungiyar tsaro na NATO zuwa yankin gabashi, yana da alaƙa kai tsaye da rikicin dake faruwa a halin yanzu a ƙasar Ukraine. Ya ce, “Ita ma tsohuwa ‘yar majalisar dokokin Amurka Tulsi Gabbard ta bayyana cewa, muddin Amurka ta yi alkawarin ba za ta shigar da ƙasar Ukraine cikin ƙungiyar NATO ba, to za ta iya kawo ƙarshen rikicin da kuma hana ɓarkewar yaƙi, amma gwamnatin Amurka ba za ta yi hakan ba. Makullin warware rikicin Ukraine na hannun Amurka da NATO.

Don haka, ina fatan Amurka da NATO, a matsayinsu na masu tayar da rikicin, za su yi tunani a kan rawar da suke takawa a rikicin na Ukraine, su ɗauki nauyin da ya dace, gami da matakai na zahiri don sassauta lamarin, da ma kawo ƙarshen rikicin ƙasar Ukraine nan da nan.”