Inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko

Da ya ke tabbatar da halin rashin kula da harkokin kiwon lafiya a matakin farko ke ciki, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na Ƙasa, Dakta Faisal Shuaib, a ranar 14 ga Fabrairu, ya ce, sama da kashi 70 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na Ƙasar (PHC) ba su da ingantattun ababen more rayuwa, magunguna da sauran abubuwan kula da lafiya.

Shuaib, wanda ya yi maganar a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumar da wata ƙungiyar farar hula ta ‘Connect Development’ (CODE), kan ƙarfafa al’amuran kiwon lafiya, ya kuma ce galibin cibiyoyin kiwon lafiya na da ƙarancin ma’aikata.

Don tabbatar da hakan, babban jami’in hukumar ta CODE, Hamzat Lawal, ya ce, PHC a Nijeriya na fuskantar ƙalubale masu tarin yawa duk da cewa su ne ke taimaka wa ɗimbin ’yan Nijeriya da ke zaune a yankunan karkara.

Da ya ke bayar da misali, Lawal ya ce, a watan Yulin 2021, CODE ta bibiyi cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 90 a cikin jihohi 15 a faɗin ƙasar nan kuma ta gano cewa kashi 80 cikin 100 na su ba su da inganci kuma ba su dace da adanawa da gudanar da allurar rigakafin Korona yadda ya kamata ba.

Lamarin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na ƙasar, a tsawon lokaci ya kasance da rashin isasssun ma’aikata, rashin ƙwararrun ma’aikata da kuma rashin magunguna da sauran kayan aikin yau da kullum.

Mu tuna cewa a shekarar 2019, ƙungiyar mata a jihar Jigawa ta ba da gudunmawar kuɗi daga cikin alawus ɗin da suka samu ƙarƙashin ‘Conditional Cash Transfer’ domin sayen motocin kai mata masu juna biyu asibiti a lokutan naƙuda. Hakan ya faru ne saboda ayyukan motar ɗaukar marasa lafiya na gwamnatin jihar ta gaza.

Wani bincike da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi a shekarar 2020 ya nuna cewa, adadin mace-macen mata a Nijeriya ya kai 814 a cikin 100,000. Wani bincike ya ce, Nijeriya da Indiya ne ke da kashi 34 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu a duniya, sai dai kuma wani rahoto a shekarar 2019 ya ce, kasadar mace-macen da mace ’yar Nijeriya ke fuskanta a rayuwa a lokacin haihuwa, bayan haihuwa ko kuma bayan varin da ciki ya kasance ɗaya daga cikin 22 cikin 100 saɓanin mutum 1.4,900 a ƙasashen da suka ci gaba.

Rahoton ya danganta mutuwar mutanen da jinkiri wajen ganowa da isa wurin kiwon lafiya, da rashin ƙwararrun jami’an da za su shawo kan lamarura da kuma rashin kayan aiki da magunguna.

Nijeriya dai ba ta kai ga yawan mace-macen yara ƙanana ba kamar yadda aka ce alƙalumman sun kai 117 cikin 1000 da aka haifa a shekarar 2019.

Wani bincike da aka yi a shekarar 2018 ya nuna cewa, Nijeriya na da jimillar cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko 34,000 domin kula da al’ummarta fiye da miliyan 200. Akwai shakku idan wannan adadi ya canja sosai a cikin shekaru uku da suka gabata.

Sai dai kuma wani abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda akasarin waɗannan cibiyoyin kiwon lafiya na cikin halin wani hali. Yana da wuya a gane cewa tsawon shekaru gwamnatocinmu sun gaza wajen samar da wannan buƙatu na yau da kullum ga ’yan Nijeriya, wanda hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Samar da kiwon lafiya na asali nauyi ne da ya rataya a wuyan jihohi da ƙananan hukumomi, amma a tsawon shekaru gwamnatin tarayya ta shiga tsakani ta hanyoyi da dama da suka haɗa da kafa hukumar kula da lafiya a matakin farko a matakin tarayya yayin da kowace jiha ita ma ta kafa nata.

Majalisar ƙasa ta 8, a shekarar 2018, ta tanadi ware kashi ɗaya bisa 100 na haɗakar kuɗaɗen shiga don magance harkokin kiwon lafiya a matakin farko.
Baya ga wannan, an yi wasu ayyukan ta hanyar shirye-shirye na ɓangarorin biyu da na ɓangarori daban-daban don bunƙasa ba da kulawar jinya a tushe. Amma duk da haka halin da ake ciki ya kasance iri ɗaya tare da babban ɓangaren jama’a da aka bari don ciyar da kan su da kuma ɗimbin yawa masu rauni ga ayyukan ma’aikatan kiwon lafiya.

A ranar 16 ga Fabrairu, 2022, majalisar dattijai ta kaɗa ƙuri’a don binciki aikin cibiyar kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa Naira biliyan 400 da gwamnatin Obasanjo ta ƙaddamar a shekarar 2006. Aikin shi ne gina cibiyar kiwon lafiya a matakin farko mai gadaje 60 a kowace daga cikin qananan hukumomi 774 na ƙasar nan. Duk da haka, yawancin ‘yan kwangilar sun yi watsi da aikin.

Blueprint Manhaja na kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su lura da irin gaza wa ‘yan Nijeriya da su ka yi wajen samar da ɗaya daga cikin muhimman buƙatun rayuwa ga talakawan Nijeriya. Lokaci ya yi da dukan waɗanda ke da alhakin su farka su yi abin da ake buƙata a gare su.

Ya kamata shugabannin siyasarmu su ji kunyar wannan gazawar, su kuma samar da hanyar ceto rayukan miliyoyin ’yan Nijeriya. Wannan shi ne abin da kowannensu ya rantse zai yi kuma dole ne su yi shi.

Haka kuma mu na kira ga kwamitin da majalisar dattawa ta kafa da ya binciki aikin kula da lafiya a matakin farko domin gudanar da aikinsa da kyau tare da tabbatar da cewa ya fallasa duk masu hannu a cikin wannan gazawar.

Lallai abin kunya ne a wannan zamani da muke ciki Nijeriya ba za ta iya ba da ingantacciyar hanyar kula da lafiya ga al’ummarta ba. Lokaci ya yi da za a canja wannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *