Sin na zage damtse wajen samar da isasshen hatsi da kauce wa sake tsunduma ƙangin talauci

Daga CRI HAUSA

Gwamnatin ƙasar Sin, ta fitar da kundi na ɗaya na shekarar 2022, wanda ya fayyace dukkanin ayyukan da za a gudanar wajen ingiza raya yankunan karkara, da tabbatar da samar da isasshen abinci, da kuma tabbatar da ganin waɗanda suka fita daga talauci ba su sake afkawa cikin ƙangin talauci ba.

Kundin na shekara shekara, wanda a bana aka fitar a jiya Talata, yakan yi nuni ga muhimman ayyukan da ƙasar ta sanya gaba. Tun daga shekarar 2004, wato shekaru 19 zuwa yanzu, fannin noma da raya karkara ne ke kasancewa a sahun farko, cikin ayyukan da kundin ke gabatarwa.

Kundin ya yi kira da a aiwatar da matakan samar da daidaito, da faɗaɗa samar da albarkatun gona, da bin dabarun yalwata kuɗaɗen shigar manoma.

Yayin taron manema labarai da aka kira a Larabar nan, ministan ma’aikatar gona da raya karkara na Sin Tang Renjian, ya ce burin Sin shi ne tabbatar da daidaito a adadin hatsi da ƙasar ke samarwa, ta yadda a duk shekara, yawan yabanyar hatsi a ƙasar zai kai sama da tan biliyan 650.

A nasa ɓangare, mataimakin daraktan babbar tawagar jami’an raya karkara na ƙasar Wu Hongyao, ya ce domin kiyaye ci gaba da aka samu a fannin rage talauci, mahukuntan Sin za su kara azama, wajen bunƙasa masana’antu, waɗanda za su yauƙaƙa kuɗaɗen shigar iyalai mazauna karkara.

Fassarawa: Saminu