Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, ta rantsar da Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da Majalisar ta tsige Mahdi Aliyu Gusau daga kujerarsa ta mataimakin gwamnan jihar.
Sanata Hassan Nasiha shi ne tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC a Zamfara.