Sin ta harba taurarin ɗan Adam biyu na nazarin yanayin samaniya

Daga CMG HAUSA

Kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan adam guda 2, na nazarin yanayin sararin samaniya da yammacin yau Litinin, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan. An yi amfani da rokar Long March-4C wajen harba taurarin na Shiyan-20 B da C, da 4 da mintuna 22 bisa agogon birnin Beijing.

Baya ga nazarin yanayin sararin samaniya, taurarin dan adam din biyu da tuni suka shiga falakin su, za su kuma gudanar da ayyukan tantance sauran fasahohi da ake amfani da su a binciken samaniya.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa