Sin: Ya kamata kwamitin sulhu ya gaggauta daidaitawa da ma ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba wa ƙasashen Afirka da ba su biya buƙatun halin da ake ciki ba

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, kwamitin sulhu na MƊD ya shirya wani taro, inda ya zartas da ƙuduri mai lamba 2588 kan takunkuman da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda ƙasar Faransa ta gabatar, ya kuma samu ƙuri’u 10 na goyon baya da kuma 5 na ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a.

Mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD, Dai Bing, ya halarci taron, inda ya ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a, kana ya yi bayani kan matsayin ƙasar Sin na ƙaurace wa kaɗa ƙuri’ar.

Dai Bing ya ce, ƙasar Sin na maraba da ƙudirin, wanda ya daidaita matakan takunkuman hana shigo da makamai da aka sanyawa gwamnatin Afirka ta Tsakiya.

A hannu guda kuma, ƙasar Sin ta yi imanin cewa, ƙudurin yana da wasu matakai na taƙaita zirga-zirga, waɗanda za su iya kawo tsaiko ga ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar Afirka ta Tsakiya ke yi, na ƙara ƙarfin tsaron ƙasar. Kuma har yanzu akwai dama ta ingantawa, har sai an dage takunkuman baki ɗaya.

Dai ya jaddada cewa, ya kamata mambobin kwamitin sulhun da abin ya shafa, su mai da hankali kan batutuwa masu ma’ana gami da buƙatun ƙasashen Afirka, da gaggauta ɗaukar matakai bisa gyare-gyaren takunkuman hana shigo da makamai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tare da yin nazari sosai kan batutuwan dake ƙunshi cikin takunkuman da aka kakabawa ƙasashen Afirka, da daidaitawa a kan lokaci da ma soke matakan takunkuman da ba su dace da buƙatun halin da ake ciki ba.

Fassarawar Ibrahim