Saƙon Sabuwar Shekarar Hijira: Adamu ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mallaki katin zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman waɗanda suka kai shekarun zaɓe da su tabbatar da sun yi rijistar katin zaɓe don su yi amfani da shi a zaɓe mai zuwa da sauransu.

Sanata Adamu ya yi wannan kira ne a wani saƙon manema labarai da ya fitar ta hannu mai taimaka masa kan sha’anin sabbin kafofin yaɗa labarai, Muhammad Nata’ala Keffi, a ranar Asabar don taya al’ummar Musulmi shiga sabuwar shekarar Musulunci, 1444.

Adamu ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga Muslimin Nijeriya da su yi koyi da karantarwar Annabi Muhammad (SAW) wajen ɗabaƙa kyawawan ɗabi’u.

Haka nan, ya buƙaci malaman Islama su yi da’awa tare da nuna wa jama’a a guji aikata duk wani abu da ya saɓa wa karantarwar Musulunci.

Daga nan, Adamu ya yi addu’ar samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a faɗin Nijeriya.