Za a gabatar da Neymar gaban kotu kan zargin zamba da cin hanci

Daga Mahdi M. Muhammad

Shekaru tara kenan da Neymar ya kammala komawa Barcelona daga ƙungiyar Santos ta Brazil. An yi la’akari da shi a matsayin matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi kyau a duniya a lokacin, sanya hannunsa ya gamu da farin ciki da yawa kuma Selecao bai yi ƙasa a gwiwa ba.

Ana zargin ɗan awallon tawagar Brazil, wanda yanzu ke taka leda a Paris St Germain da aikata zamba da cin hanci.

An daɗe ana ci gaba da shari’ar kuma a watan Oktoba ne za a fara sauraren ƙarar a kotun Barcelona.

El Pais ya yi ƙarin haske kan wasu bayanai game da shari’ar da kuma hukuncin da masu gabatar da ƙara suka yi wa Neymar da waɗanda ake zargi da haɗa baki da shi.

A ranar 17 ga watan Oktoba ne dai Neymar zai gurfana a gaban shari’a kan zargin cin hanci da rashawa, wata ɗaya kacal kafin gasar cin kofin duniya ta 2022 a Ƙatar, kuma a cewar rahoton, masu gabatar da ƙara na buƙatar kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari da kuma tarar Yuro miliyan 10.

Haka zalika, mai shigar na ƙara yana son a yanke hukunci mai tsauri ga fitaccen ɗan wasan Brazil. Suna neman kotu ta yanke wa Neymar hukuncin ɗaurin shekaru biyar, yayin da kuma suka buƙaci a dakatar da tsohon ɗan wasan na Barca shiga harkar ƙwallon ƙafa na tsawon lokaci guda.

Masu gabatar da ƙara za su kuma nemi da a yanke hukuncin ɗauri a gidan yari ga wasu tsoffin shugabannin Barca, Rossell, da Josep Maria Bartomeu, wanda shi ne mataimakin shugaban kulob ɗin a lokacin da aka kammala cinikin Neymar.