Sirikar Ganduje ta rasu

Daga Maimuna Bashir Isa

Sirikar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Hajiya Asiya Muhammad Gauyama ta rasu.

Mai taimaka wa Ganduje kan harkokin yaɗa labarai, Edwin Olofu ya yi jawabin cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce, marigayiyar ta kasance mahaifiya ga matar Ganduje, Farfesa Hafsatu Abdullahi Umar Ganduje wacce ta rasu da asubahin ranar Litinin.

Za a yi jana’izar ta a yau da misalin ƙarfe 2 na rana a gidan Ganduje da ke kan hanyar Miyangu a Jihar Kano.

Ya kuma ce wannan babban rashi ne ga iyalanta da ma duk mutanen da suka san ta, domin ta kasance jigo ce a cikin iyalanta.

Edwin ya ƙara da cewa, a madadin shugaban jam’iyyar APC’n, suna miƙa gaisuwar ta’aziyya ga Farfesa Hafsatu da iyalanta baki ɗaya gami da yin addu’a ga marigayiyar wajen fatan samun rahamar Allah.