Soja ya kashe wani mutum ta hanyar caka masa wuƙa

An samu wata yar hatsaniya a kasuwar kugbo bangaren da ake siyar da kayan gyaran mota jiya. Ana zargin wani soja ya soka wa wani mutum wuƙa, wanda sanadiyar haka mutumin ya mutu.

Kamar yadda jaridar daily trust ta gano, wanda ake zargin yan kawo gyaran motar shi ne wajen wani bakanike da ake kira yellow. Wanda daga bisani, muhawara ta shiga tsakanin su, sai sojan ya fiddo wuƙa ya caka masa.

Hakan ya jawo mutane sun lakaɗa ma sojan duka wanda ya samu ya tsere da kyar. Kuma suka ƙona motar sojan.

Komai dai ya dawo dai dai bayan yan sanda sun hallara wurin.