
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban ma’aikatan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu ƙoƙarin tada tarzoma a zanga-zangar tsadar rayuwa da ake cigaba da yi a Nijeriya, ya na mai cewa ko su janye daga yunƙurinsu ko kuma doka ta yi aiki a kan su.
Janar Christopher ya faɗi hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja game da batun zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya.
Ya ce, hukumomin tsaro musamman ƴan sanda su na ƙoƙari wajen ji da lamuran tashin-tashina a zanga-zangar, ya na mai kira ga al’ummar Nijeriya da su fahimci halin da gwamnatin tarayya ke ciki da ƙoƙarinta na bai wa al’umma damar bayyana ƴancinsu.
Ya ƙara da cewa, soji da sauran hukumomin tsaro ba za su lamunci ganin an cigaba da yamutsa al’amura a Nijeriya ba, ya na mai cewa za su ɗauki matakin doka a kan duk wanda aka kama da hannu a cikin laifin tada hargitsi.
