Sojoji ba za su saurari kiraye-kirayen kifar da gwamnatin Tinubu ba – Lagbaja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar-Gen Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa sojoji ba za su saurari kiraye-kirayen kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.

Lagbaja ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen bikin buɗe taron COAS Combined 2nd and 3rd ƙuarters a Uyo, jihar Akwa Ibom.

A cewar Lagbaja, kiraye-kirayen shiga tsakani na soji ya fi fitowa ne daga matasan Nijeriya da ba su fuskanci zamanin mulkin soja na Nijeriya ba.

Ya ce rundunar sojin Nijeriya ta gina wani sabon martaba a cikin shekaru 25 da suka gabata ta hanyar ba da damar gudanar da mulkin dimokaraɗiyya lafiya kuma ba za ta bari a yi amfani da ita wajen kawo wasu muradu a kan karagar mulki ba.

“Rundunar Sojin Nijeriya ba za ta yarda a yi amfani da ita ba wajen safarar wasu buƙatu ga mulki ba bisa ƙa’ida ba. A matsayinta na rundunar da ta fi samun karɓuwa a matsayin taɓarɓarewar ayyukan soji a baya a Nijeriya, rundunar sojin Nijeriya ba ta da niyyar rasa sabuwar martabar da ta gina a cikin shekaru 25 da suka gabata,” inji shi.

Lagbaja ya bayyana irin goyon bayan da sojoji suka samu daga gwamnati, inda ya bada misali da sayan jirage masu saukar ungulu ƙirar Bell UH-1 Huey a baya-bayan nan masu ɗauke da na’urorin zamani.

Ya kuma yi tsokaci game da jin daɗin matan da mazansu suka mutu da kuma dangin jaruman da suka mutu, wanda har yanzu yana kan hanya.

Hafsan sojin ya kuma yi jawabi ga zanga-zangar yunwa da aka yi a faɗin ƙasar a baya-bayan nan, inda ya bayyana cewa, abu ne mai buɗe ido cewa al’amuran abinci da zamantakewa na iya jefa ƙasar cikin ƙalubalen tsaro.

Ya yi alƙawarin ƙudurin sojoji na sake duba manufofinta na noma tare da samar da kariya ga manoma a cikin al’ummomin da suke noma.

Bugu da ƙari, Lagbaja ya bayyana cewa, rundunar sojin Nijeriya ta samu wasu hanyoyin yaƙi da su, irin su motocin kare nakiyoyi, bindigu, da alburusai, domin ƙarfafa ayyuka da tsaro a faɗin ƙasar nan.

By ukarofi