Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, dakarunta da aka aika garin Mangu ta Jihar Filato don magance rikicin da ke faruwa sun kashe wasu ’yan bindiga da dama.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin rundunar na intanet ta ce, lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mangu mai fama da rikicin ƙabilanci ranar Laraba.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumomin jihar sun sanya dokar hana fita ta awa ashirin da hudu a Mangu bayan ɓarkewar rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a yankin.
“Dakarun rundunar ta 3 ta sojojin ƙasa na Nijeriya da aka tura domin shawo kan rikicin da ke faruwa a Ƙaramar Hukumar Mangu ta jihar Filato sun kashe ’yan bindiga suka a yau Laraba, 12 ga watan Yuli na 2023,” in ji sanarwar Birgediya Janar Nwachukwu.
Ya ƙara da cewa, “Dakarun sun kashe masu aikata laifin ne lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton-ɓauna yayin da suka kai ɗaukin gaggawa a yankin na Mangu.”
A cewar rundunar, ta share dajin da ’yan bindigar suke samun mafaka inda ta gano bindiga uku ƙirar AK 47, harsasai 14 na musamman, babur guda ɗaya da kuma katin shaida na wani ƙaramin ɗan sanda.
Ta kammala da cewa yanzu haka dakarunta suna farautar ’yan bindigar da suka tsere ɗauke da raunukan bindiga.