Shehi Tijjani Sani Auwalun da na sani

Daga BILKISU YUSUF ALI

Duk da tunanin wasu da ke mu’amala da siyasa daga nesa ba kasafai suke fahimtar kowanne al’amari ba musamman a lissafin S’siyasar shi ya sa wasu abubuwa kan ɗaure musu kai.

Amma Wani jawabi da jagora Kwankwaso da ya yi sai na ƙara yarda da sakankacewar masu hange da tunanin Shehi Tijjani Sani Auwalu ba su san shi a Kumbotso ba lallai wancan lissafin na siyasa ya kufce musu.

Akwai yan siyasar da suka yi yaƙi na sunkuru har Allah ya tabbatar da wannan kujerar ta Abba Wanda Shehu Tijjani yana ciki.

Ba ma iya yaƙin ba tun a baya ya sadaukar da takararsa ta gwamna a 2019 ya marawa Abba baya duk kuwa da cewa a lokacin ya zagaya ƙananan hukumomi 44 don shiga zaɓe.

A siyasanice, Shehu Tijjani ba yankan rake ba ne ya yi takarkari kama da gwamna da Neman majalisar tarayya. A wannan karon kuwa babu babbar Zawiyya da Shehu bai Taka ba a ƙananan jukumomi 44 na jihar Kano don neman goyon bayan al’umma kan su zaɓi Abba baya da tarurruka na ƙungiyoyi na kwankwasiyya duk dai don nasarar zaɓe.

A ɓangaren ofishinsa kuwa da yanzu yake shugabanta batun ka ce ya cancanta ma ba ta baki ne. Na farko dai tsatson da ya fito na Shehu Ibrahim Inyas kaɗai ya Isa wakiltar Musulunci a faɗin duniya ba wai iya Kano ba.

Gogayyarsa da yawon neman iliminsa na addini da na boko ya zama hujjar tafiyar da ofis ɗinsa ba hamayya. Haƙuri da juriyarsa da fadin gaskiya a kan kowa da jajircewarsa a duk abin da ya sa gaba shi halinsa ne mai buƙatar tabbatarwa ya kalli ƙungiyarsa ta TIGMEIN Wanda shi kaɗai ya zagaya dukkan Nijeriya Wanda a yau dai a Tijjaniyya babu ƙungiya me karfinta da taimakon al’umma kuma ba iya yan Tijjaniyar ba kamar ita.

Ita TIGMEIN babbar manufarta ita ce ma taimakon Al’umma Wanda kuma Ana nan duk ƙasar nan Ana kan yi. Sannan bayan TIGMEIN A kalli Majma’u Ita ma ta kasa ce kuma da tallafinsa ta ginu.

Don haka Shehi Tijjani yasan Makamaf aiki yasan yadda ake hulɗa da jama’a. Tijjaniyya kuwa da ma wannan kayansu sai dai addu’a Allah Ya ƙara kusanci. Fatanmu Shehu Tijjani ya kasance a Shehun nan da muka sani wanda duk wanda ya yi mu’amala da shi zai ce sam-barka.

Yana cikin mutane ƙallilan da a yau da a nuna kan son taimakon matasa, don haka matasa a wannan ofishin su ma suna da gurbi na musamman Ina da yaƙinin duk kukansu in dai ya shafi ofishinsa to ba je ka ka dawo. Don kuwa inda aka San darajar goro nan ake yayyafa masa ruwa.

Gwamnan Kanawa muna godiya da zaɓen da ka yi mana na gwarzo abin alfahari, tabbas an ajiye k’ƙwarya a gurbinta. ‘Yan ƙaramar hukumar Kumbotso congratulations!

Kwamishinan Addinai Shehi Sani Auwalu Ahmed Tijjani Allah Ya riƙa, Allah Ya kare ka karewa Allah ya yi riƙo da hannayenka, amin .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *