Sufeton ‘yan sandan Nijeriya ya tura ƙarin dakaru Ribas bayan kisan ɗan sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya ya yi tir da kisan jami’n rundunar da aka yi a jihar Ribas sakamakon rikicin siyasar da ke ci gaba da ruruwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce IGP Kayode Egbetokun ya bai wa kwamashinan ‘yan sandan jihar umarnin tsaurara tsaro don gano waɗanda suka aikata kisan.

Sanarwar ta ce an kashe Sufeto Daɓ id Mgbada da kuma wani ɗan sa-kai Samuel Nwigwe a rikicin da ya auku tsakanin magoya ɓ angarorin biyu bayan Gwamna Fubara ya rushe shugabannin ƙananan hukumomi tare da maye gurbinsu da na riƙo.

“Sakamakon haka, IGP ya aika da dakarun rundunar na Intelligence Response Team (IRT) domin su taimaka wa ‘yansandan Ribas wajen kama makasan,” in ji sanarwar.

A ranar Laraba ne gwamnan ya rantsar da shugabannin bayan tun da farko majalisar dokokin jihar, ɓ angaren da ke biyayya ga gwamnan, ya tantance mutanen kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.