Sulhu: Atiku ya fatattaki su Ganduje, ya ce da masu daraja zai zauna

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Wazirin Adamawa kuma ɗan takarar Jam’iyyar PDP a zaven 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya fatattaki tawagar neman sulhun da zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya mai jiran gado, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya aike masa, wacce ta ƙunshi Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan na Kebbi Atiku Bagudu, na Jihar Jigawa Badaru Abubakar da na Jihar Nasarawa Abdullahi Sule tare da tsohon Shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu.

Majiya mai tushe daga jikin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ta shaida wa News Point Nigeria cewa, nan take Atikun ya ja kunnensu da kada ya sake ganin ƙeyarsu a gidansa, la’alla an yi sulhu ko ba a yi ba, kuma yana nan akan bakansa na garzaya wa kotu, don neman haƙƙi.

Majiyar ta ce, “har yanzu Waziri a fusace ya ke, amma ya amince ya gana da su, sai dai kuma Ina tsammanin ’yan tawagar ne suka qara fusata shi. Kamata ya yi Asuwaju ya aike da wasu mutanen, ba waɗannan ba; mutanen da ba su da hannu a cikin zaɓen.”

Ta cigaba da cewa, “a halin da ake ciki a fusace ya ke da wasu daga cikin gwamnonin. Don haka tura irin waɗannan mutanen a fili ta ke cewa ba tunani ne mai kyau ba. Bugu da ƙari, Waziri ya yanke shawarar zuwa kotu, kuma zai yaqi nasarar Tinubu har zuwa ƙarshen lamarin.

“Ya yi zama da yawa tare da masu ruwa da tsaki, jagororin jam’iyya da wasu ƙungiyoyin ƙasashen duniya, kuma a dukkan ƙashen ganawar matsaya ɗaya ce- kotu.

“Idan ma akwai yiwuwar sasanci a tsakani, Ina ganin Tinubu ne kaɗai zai sa hakan, kuma shi ya san Waziri sosai, sannan ya san abinda zai iya yi.”

Idan za a iya tunawa, a ranar Laraba Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ne sanar da cewa, Tinubu ya kafa kwamitin sasanci tsakaninsa da ’yan takarar shugaban ƙasa, kamar yadda Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Richard Olatunde, ya sanar.

A safiyar ranar Laraba ne dai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da Tinubu ya lashe zaɓen da ƙuri’u 8,794,726, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu 6,984,520, shi kuma Peter Obi na LP ya samu ƙuri’a 6,101,533, sannan Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ya samu 1,496,687. Amma sai dai bakiɗayan su ukun suka yi tir da wannan sakamakon zaɓen.