Surukar Mataimakin Shugaban Ƙasa ta rasu

Surukar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Hajiya Maryam Albishir, ta rasu a jiya lahadi bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Mai magana da yawun da Mataimakin Shugaban ƙasa Stanley Nwkocha ne ya fitar a wata sanarwa ranar Litinin. Mr Nwkocha ya ƙara da cewa za a yi jana’izar ta da yammacin ranar Litinin a jihar Kano kamar yadda musulunci ya tanada.

Marigayiyar an mata shaida a matsayin mutum mai jajircewa da tausayi.