Ta haifi ’yan tara a haihuwa ɗaya

Wani abin al’ajabi ya faru yayin da wata mata ’yar ƙasar Mali mai suna Halima Cisse mai shekara 25 ta haifi jarirai tara, lamarin da ya girgiza likitoci duk da irin binciken da suka gudanar kafin haihuwarta.

Halima, ta haifi jariran tara ne a ƙasar Maroko. Gwamnatin Mali ta ɗauki nauyinta domin samun kulawar kwararrun likitoci.

“Na yi farin ciki sosai,” kamar yadda mijinta ya shaida wa manema labarai.

Ya ce, “matata da jariran da aka haifa (mata biyar da maza huɗu) suna cikin ƙoshin lafiya”.

A shekarar 2009 wata ta haifi jarirai takwas a Amurka, kuma ita ce ke riƙe da kambun kundin tarihi na duniya na wadda ta haifi jarirai mafiya yawa a lokaci guda, sannan suke cikin koshin lafiya.

A baya an tava samun wasu mata da suka haifi jarirai takwas a lokaci ɗaya.

Wata ta haifi ’yan takwas a Ostireliya a 1971, sai wata mata a Malesiya da ta haifi ’yan takwas a 1999, amma babu ɗaya daga cikin jariran da ya rayu bayan kwanaki da haihuwarsu.

Nadya Suleman, ita ce ke riƙe da kambun tarihi na duniya wajen haihuwar yara da yawa lokaci guda, yanzu haka yaran sun girma inda suka kai shekara 12 a duniya. Ministar Lafiya ta Mali, Fanta Siby ta taya ayarin likitoci a Mali da Maroko murnar yadda suka yi hidima har matar ta sauka lafiya.

Daraktan Kiwon Lafiya na Asibitin Ain Borja, Farfesa Youssef Alaoui da ke Kasabalanka, inda Misis Cisse ta haihu, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, ba kasafai ake samun mace ta haifi jarirai haka ba, inda ya ce abin ban-mamaki ne, kuma likitoci 10 da ma’aikatan lafiya 25 ne suka taimaka wajen haihuwar matar.

Nauyin jariran ya kai tsakanin giram 500 zuwa kilo ɗaya, kuma ya ce za a ajiye su a cikin kwalbar kula da jarirai na tsawon wata biyu zuwa uku. Juna biyun Misis Cisse ya zama abin tsegumi a Mali duk da cewa gwajin da aka yi mata a farko-farko ya nuna jarirai bakwai ta ke ɗauke da su, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana.

Likitoci a ƙasar da ke Afirka ta Arewa sun damu da yanayin kulawar da za ta samu bayan haihuwar jariran, hakan ne ya sa gwamnatin ƙasar ta kai mata ɗauki tare da fitar da ita zuwa qasar Maroko don ba ta kulawa ta musamman.

Bayan shafe mako biyu a wani asibiti a Bamako, babban birnin ƙasar Mali, an yanke shawarar mayar da Misis Cisse zuwa Maroko a wancan lokacin, kamar yadda Dokta Siby ta shaida wa Reuters.

Bayan shafe mako biyar a wani asibitin ƙasar Maroko, ta haihu a wani sashen kulawa na musamman a ranar Talata, inji Ministar.

A cewar Farfesa Alaoui, Misis Cisse na ɗauke da juna biyu na mako 25 lokacin da aka kwantar da ita a asibitinsu kuma likitocinsu sun yi nasarar tsawaita wa’adin cikin zuwa mako 30.

Mijinta Kader Arby, ya ce, “Allah ne Ya ba mu waɗannan yara, Shi ne Ya san me zai same su, ban damu da abin da zai faru ba, idan Ubangiji Ya yi ikonSa, akwai dalili”.

Ya ce, ya ji dadin tallafin da iyalansa suka samu bayan haihuwar matar tasa.

“Kowa sai kirana ya ke yi! Kirana kawai ake yi! Hukumomin Mali sun kira ni a waya sun nuna farin cikinsu. Na gode musu. Shugaban Ƙasa da kansa ma sai da ya kira ni ya min murna,” inji shi.