Taimaka wa jami’an tsaro gano maɓoyar ɓata-gari

Daga ABBA YAKUBU ABDULLAHI

A yayin da na ke wannan rubutu rahotanni na bayyana cewa, kawo yanzu a na cigaba da gano wasu manyan masu aikata laifi da suka tsere daga gidan Gyara Halinka na Kuje da ya ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, sakamakon harin da aka ɗora alhakin sa kan ƙungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP, waɗanda aka ce sun je ne domin kuɓutar da wasu ‘yan uwansu da ke tsare a gidan yarin su kimanin 64. Bayan waɗanda aka je kuvutarwa har da ƙarin wasu vata gari da suka yi amfani da wannan dama suka tsere.

A sanarwar da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya fitar ya bayyana cewa, ana kyautata zaton waɗanda suka gudu sun kai 879, sannan kuma yayin wannan rubutun an samu nasarar dawo da wasu fursunonin su 443. Wannan na nufin kenan akwai wasu manyan masu aikata laifi da suka kai kimanin kashi hamsin da ba a gano su ba, za kuma su shiga cikin jama’a ne su ci gaba da aikata ɓarna da ƙara dagula harkokin tsaro.

Taimakon da wasu ‘yan ƙasa nagari suka bayar wajen samar da bayanan sirri da suka taimaka wajen sake dawo da wasu daga cikin vata garin da suka tsere kurkukun Kuje ya ƙara nuna tasirin da bayanan da jama’a ke bayarwa wajen daƙile ayyukan ɓata gari. Ko da ya ke sau da dama wasu na nuna tsoro ko fargabar fitar da bayanan sirri, don kada a tona asirin su ga maƙiya daga baya su biyo baya su cutar da su. Amma fitar da bayanan da za su ceci rayukan jama’a da dama na da matuƙar muhimmanci, don haka shiru da kawar da kai ba zai yi magani ba, domin wani lokaci illar hakan na iya dawowa ta shafi kai da ka ƙi yin magana ko ɗaukar mataki. 

Haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda da jama’ar gari ko farar hula wajen inganta aikin samar da tsaro a cikin al’umma ya fara ne tun a shekarar 2004 sakamakon yadda aikata laifuka ya yi tsamari a tsakanin al’umma tun a wancan lokacin. Don haka aka ƙirƙiro da rundunar ’yan banga, waɗanda suke zaɓaɓɓun mutane ne daga cikin al’umma da suka amince su ba da lokacin su da rayuwarsu, don samar da kariya a cikin al’ummarsu. Ba wai don sun zama ‘yan sanda ba, amma saboda kusancin su da jama’a, za su iya riga jami’an tsaro saurin samun bayanai da gano maɓoyar ɓata gari da duk wasu lunguna da ake aikata rashin gaskiya, da kuma kai ɗaukin gaggawa, kafin jami’an tsaro su kai ɗauki daga baya. 

Wannan ƙawance tsakanin amintattun cikin jama’a da jami’an tsaro yana da muhimmanci sosai wajen inganta tsaro, samar da yarda a tsakanin jama’a da hukuma, da haɗa ƙarfi waje guda don a yaƙi masu aikata ɓarna. Tsarin har wa yau na koyawa jama’a sanin muhimmancin ba da gudunmawa a matsayin su na ‘ya’yan al’umma, waɗanda suke da haƙƙin sa ido su ma kan abubuwan da ke faruwa a maƙwabtansu. 

Ko da ya ke a farko, an yi zargin su waɗannan ‘yan banga za su iya wuce gona da iri wajen ɗaukar doka a hannu, ko a haɗa baki da su da ɓata gari a aikata wata ɓarna, da kuma zargi wasu mambobinsu na iya zama tsoffin masu aikata laifuka ne da suka tuba, don haka za su iya sanya son zuciya a cikin aikinsu. 

A shekarar da ta gabata ta 2021 cikin watan Oktoba, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da amfani da sabon tsarin ‘Yan Sandan Al’umma da za a ɗauka aiki ƙarƙashin jagorancin Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa tare da sanya hannu don cire kuɗi Naira Biliyan 13 da Miliyan 3 domin fara gudanar da wannan aiki, wanda bai samu bayyana ‘yan Nijeriya su tabbatar da abin da ake faɗa ba sai a cikin ‘yan makwannin nan, inda aka fitar da sabbin jami’an ‘yan sanda, kimanin dubu 20, domin a ƙara kan adadin jami’an ‘yan sandan da ake su a ƙasar nan, waɗanda aka daɗe ana kukan sun yi ƙaranci. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara kiraye kirayen ‘yan sanda su riƙa canja salon yadda suke mu’amala da mutane, don su bai wa jama’a damar sakin jikinsu su da jami’an tsaro har su iya shaida musu abin da suke nema na daga bayanan sirri. 

A sakamakon yadda ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram suka tsananta musamman a yankin Arewa maso Gabas a shekarun baya, gamayyar matasan Borno sun yunƙura don kare kansu da ba da gudunmawa wajen samar da tsaro a yankunansu, ta hanyar ɗaukar gorori da adduna domin farautar ‘yan Boko Haram, wannan yunƙuri shi ya haifar da abin da a yanzu ake kira da Sibiliyan JTF, wato gamayyar ƙungiyoyin matasa, ‘yan banga da maharba, don a tallafawa jami’an tsaro da ke yaqi da ‘yan ta’adda. 

Wannan tsari ya samu goyon bayan matasa daga sassan ƙasar nan daban-daban, musamman a jihohin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro irin su Kaduna, Katsina, Zamfara, Adamawa, Filato da Naija, saboda su ma su taimakawa jami’an tsaro a yankunansu. Ko da ya ke lokaci zuwa lokaci an sha samun rashin jituwa tsakanin waɗannan matasa da jami’an tsaro, ko jama’ar gari, inda har gwamnatocin wasu jihohin suka kafa dokokin haramta ayyukan ‘yan sa kai saboda yadda ake samun rahotannin ƙorafe-ƙorafe na ɗaukar doka a hannu ko haɗa ɓata gari. 

A ‘yan shekarun baya wasu rahotanni sun bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da Jihar Zamfara ke fuskanta gwamnatin jihar ta ɗauki ‘yan ƙato da gora 500 a kowacce masarauta cikin masarautu 17 na jihar, wanda yawansu ya kai 8, 500 kuma tana biyansu Naira dubu 15 a kowanne wata duk domin inganta tsaro da kwanciyar hankali a jihar.

Wannan yunƙuri na gwamnatin jihar ya taimaka ainun sakamakon yawaitar yadda ake garkuwa da mutane a wasu wurare kan hanyar Zamfara zuwa Sakkwato, ‘yan kato da gora wato Civilian JTF da gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauka na ba da tsaro iya gwargwado, duk kuwa da ƙalubalen rashin makaman da za su iya tinkarar ‘yan bindiga, da kuma rashin gogewa.

Sai dai kamar yadda muka ji a rahotanni a ‘yan makwannin da suka gabata gwamnatin jihar ta ba da umarnin rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tantance duk mutanen da ke da buƙatar a ba su dama su mallaki ƙananan makamai don kare kansu, domin ba su dama, saboda yadda sha’anin taɓarɓarewar tsaro ya ke ƙara dagulewa a jihar, da ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga. Da zargin da ake yi wa wasu ‘yan ƙato da gorar da haɗa baki da vata garin wajen sayar da bayanan sirri.

Yana da kyau gwamnati ta samar da kyakkyawan tsari na horar da waɗannan matasa ‘yansa kai, tsakanin ‘yan banga da maharba, don ƙara sanin dokokin aiki da amfani da makamai yadda ya kamata, a kuma samar musu da alawus-alawus na ƙarfafa gwiwa ba wai a bar su haka kara zube ba, yadda zuciyarsu za ta kai su ga ba da kai bori ya hau a wajen ‘yan ta’adda. 

Kamar yadda muka sha ji daga bakin wasu irin ‘yan ta’addan da suke naɗar muryoyinsu suna isar da saƙonni ga jama’a ko a hirarraki da a kan yi da su, inda suke kokawa da karon su da ‘yan banga ko mahara, saɓaninsu ji tsoron hukuma. Abin da ke nuna tasirin ayyukan ‘yan bangan yana haifar musu da cikas. Ashe kuwa tun da muka fahimci haka ya kamata mu ƙarfafa musu gwiwa, ta hanyar samar musu da kayan aiki na zamani, horar wa, motocin aiki da sauran abubuwan da za su sa ayyukan ‘yan ƙungiyarsu samu nasara. 

Jama’a su ma yana da kyau su fahimci cewa aikin tsaro na kowa da kowa ne ba sai ɗan banga ko ɗan ƙato da gora ba. Mu yarda cewa, ‘yan sanda ko sojoji da sauran jami’an tsaro ba za su iya yi maganin tsaro ba, sai mu da kan mu mun taimaka musu da bayanai da shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye al’ummarmu.

Mu sanya a ran mu cewa, kowannen mu ɗan sanda, a cikin gidajen mu, makwaftan mu, unguwanni mu, duk wani motsi da muka ji ko gani wanda ba mu yarda da shi ba to, lallai mu hanzarta kai rahoto ga wani ofishin jami’an tsaro mafi kusa.