Buhari bai ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu wa’adin magance yajin aikin ASUU ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, babu inda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu wa’adin makonni biyu a kan ya magance matsalar yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ta ƙi ce, ta ƙi cinyewa.

Fadar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, a ranar Laraba.

A Talatar da ta gabata wasu rahotanni suka ce, bayan da Shugaba Buhari ya saurari hukumomin da ke faɗi-tashin ganin an magance wannan yajin aikin, sai ya bai wa Minista Adamu Adamu wa’adin makonni biyu a kan ya kawo ƙarshen yajin aikin don jami’o’i su koma aiki.

Kalzalika, rahotannin sun ce wai Buharin ya umarci Ministan Ƙwadago a kan ya cire hannunsa daga sha’anin tattaunawar da ake yi da ASUU.

Sai dai, Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton inda ta ce babu inda Shugaba Buhari ya bai wa Ministan Ilimin wa’adin kawo ƙarshen wannan yajin aiki.

Fadar ta ƙara da cewa, yadda zancen yake shi ne, yayin taron Majalisar Zartarwa Ministan Ilimi ya roƙi Ministan Ƙwadago ya zame hannunsa daga tattaunawar da ake yi da ASUU don shi ya ci gaba da jan ragamar tattaunawar don kammala abin da ya soma.

Don haka Fadar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa labaran da ba su dace ba a cikin al’umma.

Kimanin wata shida kenan da ASUU ta soma wannan yajin aikin wanda har yanzu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.