Ƙasar Sin za ta tsaya kan manufar buɗe ƙofarta ga duniya

Daga CMG HAUSA

Firaministan ƙasar Sin mista Li Keqiang ya ce, tattalin arzikin ƙasarsa ya haɗe da na duniya cikin wani matsayi mai zurfi, kana buɗe ƙofarta ga duniya wata babbar manufa ce ta ƙasar. Saboda haka, Sin za ta tsaya kan wannan muhimmiyar manufa, gami da ƙoƙarin inganta harkoki a wannan fanni.

Mista Li ya faɗi haka ne a jiya Talata, yayin da yake halartar taron manyan ‘yan kasuwan kasashe daban daban ƙarƙashin laimar dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, wanda ya gudana ta kafar bidiyo.

A cewar firaministan ƙasar Sin, manufar buɗe kofar kasar ta shafi ƙasashe masu sukuni, da waɗanda ke kan hanyar tasowa. Sa’an nan ƙasar Sin za ta ci gaba da kokarin kare tsarin ciniki da ya shafi ɓangarori daban-daban, da Ƙungiyar Ciniki ta Duniya (WTO) take jagoranta, da sa ƙaimi ga yin cikin ‘yanci da adalci.

Firaminista Li ya ƙara da cewa, ƙasarsa za ta ƙara ƙoƙarin daidaita muhallin gudanar da harkokin kasuwanci, da ɗaukar matakan kandagarkin annobar COVID-19 masu dacewa, da kyautata yanayin ayyukan samar da izinin shiga ƙasar, da gudanar da gwajin kwayoyin cutar COVID-19. Haka kuma za ta taimakawa mutanen da suke neman yin ciniki ko aiki a ƙasashen ƙetare, don inganta mu’ammalar jama’ar Sin da ta kasashen waje.

Ban da wannan kuma, babban jami’in ya nanata cewa, ƙasar Sin za ta kiyaye manyan manufofinta na yanzu, don tabbatar da cimma burinta na raya tattalin arziki zuwa wani matsayin da take bukata, a wannan shekarar da muke ciki. Ya ce, sabon zagayen yaɗuwar cutar COVID-19 a duniya gami da sauran abubuwan da ba a iya hasashensu ba, sun sa tattalin arzikin Sin fuskantar matsi.

Duk da haka, a cewar firaministan, matakan daidaita yanayin da gwamnatin ƙasar Sin ta dauka, musamman ma waɗanda suka shafi ba da tallafi ga kamfanoni, da shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, sun yi amfani, inda suka sanya tattalin arzikin ƙasar komawa yanayi na ƙaruwar, sai dai kuma ana buƙatar daukar karin matakai don tabbatar da ɗorewar yanayin.

Fassarawar Bello Wang