Tantance ’yan takara: Masu nagarta kawai APC za ta tsayar a 2023, inji Adamu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya tabbatar da cewa, jam’iyyar za ta tsayar da ’yan takara masu nagarta ne kawai da za su iya samun tikitin tsayawa takarar muƙamai daban-daban na jam’iyyar APC a babban zaɓen 2023.

Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da kwamitocin tantance masu neman tsayawa takarar gwamna, sanata da na majalisar wakilai na jam’iyyar a Abuja a ranar Asabar, 14 ga Mayu, 2022.

Shugaban na ƙasa wanda Malam Abubakar Kyari ya wakilta, ya kuma yi amfani da wannan damar wajen maraba da sabbin waɗanda suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.

Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Suleiman Argungu, ya ce, jam’iyyar tana da jimillar ’yan takarar sanata 145 yayin da 1,197 ke neman kujerar majalisar wakilai.

Kwamitin maraba da ku baki ɗaya. An yi wannan ne domin tantance ‘yan takararmu na gwamna da ‘yan takarar sanata da ‘yan takarar majalisar wakilai.

“Har ila yau, muna da ƙa’idojin tantance masu neman takara da fom na tantancewa da za a baiwa kowane kwamitin tantancewar. Muna sa ran za a yi wannan aiki tsakanin yau da gobe. Mun yi imanin wannan ba zai zama wani babban aiki a gare mu ba, kuma muna addu’ar a yi wa duk masu son tsayawa takara adalci domin a shekarar 2023 za mu samu nagartattun ‘yan takara masu nagarta da za su yi takara a kan dandalin babbar jam’iyyarmu.”

Argungu ya bayyana cewa, “har yanzu muna da ’yan takarar shugaban ƙasa 28. Za a tantance su a ranar 23 ga Mayu, 2022.”