Tarihin kasuwanci a Kano (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A farkon shekara ta 1496 miladiyya, Sarkin kano Muhammad Rumfa ya yi waɗansu baƙin fataken Turawa da suka ɓullo daga Kumasi ta ƙasar Gwanja (Ghana) can yamma da Ilorin.
A harshen Hausa muna kiransu da suna Patoki, amma ainihin sunansu Portuguese, ma’ana mutanen ƙasar Portugal. Babban cinikin waɗannan Turawan shi ne fataucin bayi, sune Turawan farko da suka kawo gyaɗa garin Kano.

Su kan sayi bayi maza da mata a kasuwa. Su kuma sukan sayarwa da Kanawa gyada. Yayin da suka kammala sayar da gyaɗar tasu, sai suka shirya bayin da suka saya, suka tashi suka koma ta gwanja, sannan suka yi kudu suka riski birnin Ankara wanda ya ke a ƙasar Turkey a yau, sannan suka hau teku da bayinsu su ka yi yamma sosai har zuwa wata ƙasa mai suna Brazil wadda ke jikin Amurka ta Kudu. Anan ne kasuwar da suke sayar da bayin nasu ta ke.

Haka kuma, a shekara ta 1497, waɗansu Larabawa sun zo Kano daga ƙasar Casabalanca ta Morocco. Sun sauka a wurin ’yan uwansu da ke zaune anan dandalin Turawa cikin birnin Kano.

Daga cikin gaisuwar da Waɗannan Larabawa suka kawowa Sarki Rumfa, akwai Saihanai babba da ƙarami. An ce sarki ya tambayesu menene sunan wannan mazubin ruwan? Sai suka ce masa sunansa Saihan. Daga nan sai ya kira wani bawansa mai suna Santali, ya ce masa ga waɗannan Saihanai nan, ɗaya ka kai min gida saboda alwala, ɗayan kuma ka riqa bina da shi da ruwa koda zan buƙace shi. Tun daga nan ne sunan Santali ya zama sunan Sarauta.

A dai cikin wannan shekara ne aka ce fataken nan ’yan ƙasar Girka sun sake komowa Kano, inda sarki ya sake zaunar da su a unguwar da Rijiyar ’Yar Akwa ta ke, watau masaukinsu na farko kenan.

An ce, su ne suka kawo wani irin kuɗi na azurfa Kano, a jikin kuɗin an zana suna kamar haka Mary Treesa Dollar.
Da irin waɗannan kuɗin ne kuma fataken suka riƙa sayen bayi a kasuwa, da kiraza, albasa da sauran kayayyaki. Irin waɗancan kuɗin ne kuma mata suka riƙa haɗawa suna rataya wa ’ya’yansu a wuya. Wata macen takan haɗa kamar uku ta ɗaura, watakuma biyar, gwargwadon arzikinta. A wannan zamanin, sarkin Kano muhammadu Rumfa naɗa kimanin shekaru talatin bisa gadon mulkin Kano.

Kasuwa dai wurin haɗuwa ce ta dukkanin mutanen gari ko alƙarya, wacce ta ke samar da kayayyakin amfanin jama’a na yau da kullum. A zamanin-da, kasuwa na zamowa a matsayin hanyar sadarwa ko cibiyar watsa labaran da suka shafi jama’ar gari.

A nan ƙasar Hausa, wurin kasuwa yakan zamo na wucin gadi, wanda za a iya zuwa lokaci zuwa lokaci, ko kuma na dindindin.

Kasancewar Kano a tsakiyar ƙasar Hausa tun asali, ya sa har abada ta ke alfahari da manyan kasuwanninta a tarihin harkar kasuwancin ƙasar Hausa.

Tsofaffin kasuwanni da suka fara kafuwa a cikin birnin Kano sun haɗa da kasuwar Kurmi, kasuwar Sabon Gari, kasuwar Rimi. Daga nan sai irinsu kasuwar Kwari da kasuwar ’Yan Awaki, kasuwar Ƙofar Wambai da sauransu.

A shekara ta 1445 miladiyya aka ce Sarkin Kano Abdullahi Burja, ya kafa sabuwar doka akan masu tallan bayi maza da mata, inda ya ce, su daina yawo suna wahalar dasu wajen talla a cikin birni, sai dai su fita can wajen gari kudu da tsohuwar unguwar Mandawari domin akwai manyan bishiyoyi masu inuwa a ko ina a wurin, su riƙa zama suna saye da sayarwar bayin.

Wannan wurin shi ne gabas da ofishin wakilin Yamma. Yana nan kuma har yanzu a unguwar Magashi, sai dai yanzu gidaje ne a wurin. Shekaru 570 kenan.

An kafa kasuwar Kwari a zamanin sarkin Kano Muhammadu Rumfa, shekara ta 1463 miladiyya, amma an ce akwai kasuwar KARAFKA wadda ta wanzu tun shekara ta 1438.

An sake gina kasuwar Kurmi a shekarar 1912 miladiyya da ƙayataccen ginin ƙasa irin na wancan zamanin mai rufin ƙyami. An ɗauko qyamin ne daga Tudun wadar ɗan kadai ta gabashin kano, waɗanda suke ɗaukowar kuwa ɗaurarrun ne ’yan kurkuku, kuma a ƙafa su ke zuwa su ɗauko, yayin da masu gadinsu ke biye dasu a kan jakuna.

Kamar yadda Tarihi ya nuna, ita wannan kasuwa ta samo sunanta ne daga Rafin Jakara inda mutane suka fara zama a Kano suna yin farauta a wani kurmi kusa da rafin, don haka har yanzu sunan Jakara bai ɓata ba, yayin da kasuwar kurmi kuma ta zamo anan kusa da unguwar Jakarar.
A zamanin da wannan kasuwa ta kafu, an soma kakkafa rumfunan zana ne a cikinta domim aiwatar da harkar kasuwanci, kuma an tsara yadda kowanne mai sayar da kaya zai zauna a rumfarsa don gudanarwar kasuwancin.

Daga baya ne Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya bada Umarni aka soma gine-ginen daɗe da siminti a cikinta. An ce wasu Turawa watau Moge, Borkon, da Dogon Lamba sune suka tsara gine-ginen domin sarrafa harkar kasuwanci a cinin kasuwar.

A zamanin mulkin sarakunan ƙasar hausa kafin zuwan Turawa, mutane basa fitowa da kaya barkatai a rumfar kasuwa, sai dai idan baƙo ya zo yana son sayen kaya masu yawa a tafi da shi gida a ba shi iya abinda ya ke so ya tafi da shi ƙasarsa.

Amma dai an samu cewa kasuwar Kurmi ta riƙa kardar fatake daga manyan garuruwan ƙasar Hausa da makwabta, harma da Larabawa. Kayan koli kuma shi aka fi sayarwa a cikinta.

A wata faɗar kuma an ce, tun zamanin sarkin Kabo Muhammadu Rumfa akwai kasuwar Kurmi. An ce yana da shekara 24 bisa gadon sarauta ya yi hawa, ya tafi Kurmin Jakara tare da hakimansa da bayi da kuma ma’aikata ɗauke da kayan aiki, sannan ya nuna tun daga tsakiyar fadamar Jakara, ɓangaren gabas, aka yi ta saran itatuwa har sai da aka samar da sarari gagarumi. Daga nan da ya ke an ce shi gwanin bin tarihi ne, kima ya samu cewa a lokacin Sarkin kano gijimasu, madakin Kano ke kula da harkar kasuwanci, sai shima ya naɗa madakinsa domin yayi wa kasuwar gine-gine tare da haɗaka ta.

Tun daga wancan lokacin kuwa kasuwar ke haɗaka, har zuwa yau.

Wannan shi ne abinda ya samu dangane da tarihin kasuwanci a Kano.