Takaicin rayuwar aure cikin uƙuba

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata, na halarci wani taron Muhadara da wata ƙungiya a Jos ta saba gudanarwa duk shekara cikin watan Ramadan, inda aka saba gayyatar malamai daga ɓangarori daban-daban suna faɗakarwa kan wasu muhimman darussa da suke ci wa jama’a tuwo a ƙwarya. Domin fitar da wani tsari ko wasu shawarwari da al’umma za su inganta rayuwar su a kai cikin sauran ragowar watannin shekara.

A bana Muhadarar ta mayar da hankali ne wajen duba matsalolin auratayya da ƙalubalen rabe raben aure a tsakanin al’ummar musulmi Hausawa, da kuma tattauna ƙalubalen da al’ummar Musulmin Jihar Filato ke fuskanta a siyasance. Amma abin da na ke son yin tsokaci a kai a wannan mako shi ne batun muhimmancin kafa cibiyar kula da koke-koken ma’aurata da faɗakar da sabbin ma’aurata ƙa’idojin zamantakewar aure a bisa koyarwar addinin Musulunci, wanda wannan ƙungiya mai suna Abba Na Shehu Community Development Initiative Forum a turance, da haɗin gwiwar ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam suka amince za su kafa, domin taimakawa wajen rage yawan kisan aure da ake samu tsakanin Musulmi, wani lokaci ma kan wata matsala da ba ta kai ta kawo ba.

Ɗaya daga cikin shugabannin taron wanda kuma Alƙali ne a kotun yanki ta cikin garin Jos, mai shari’a Ghazali Isma’il Adam, na’ibin Babban Limamin Jos, ya bayyana cewa, cikin shekara guda kimanin kashi 90 cikin ɗari na ƙararrakin da kotun ta saurara sun shafi matsalolin auratayya ne, kuma mafi akasari daga Hausawa Musulmi ne, ɗaya daga ciki ma da ta kai ga rabuwar aure don takaici, ta fara ne daga saɓani kan zarmewar gishiri a cikin miya!

Duk da ƙoƙarin da ofisoshin Jama’atu Nasril Islam a matakin Jihar Filato da ƙaramar hukumar Jos ta Arewa suke yi wajen sauraron koke-koken aure da sulhunta saɓanin ma’aurata, malaman na ganin lallai akwai buƙatar samar da wata cibiya ta musamman da za ta riƙa shiga tsakani, don kashe wutar rikicin da ake yawan samu a gidajen aure da shiryawa sabbin angwaye da amare bita, don shiga gidajen aure cikin ilimin sanin haƙƙoƙi da ƙa’idojin zaman gidan aure. Shawarar da ta samu goyon bayan akasarin mahalarta Muhadarar, wanda kuma nan take aka kafa kwamitin da zai yi nazari kan tsarin ayyukan cibiyar.

A yayin da wannan ƙungiya da haɗin gwiwar malamai ke ƙoƙarin ceto rayuwar ma’aurata a Jos, a wasu sassan Nijeriya ma haka wannan matsala ta ke cigaba da zama barazana ga zamantakewar iyali inda ake hasashen Jihar Kano ce ke kan gaba a tsakanin jihohin arewacin ƙasar nan. Kamar yadda wani rahoton da tashar talabijin ta Aljazeera ta wallafa ke nuni da cewa, a duk aure uku da aka ɗaura, ɗaya na mutuwa kafin shekara ta zago. Ƙiyasin da aka ce ya haura na kowacce ƙasa a yankin Afirka ta Yamma.

Dalilan da ke haddasa rabuwar aure na da yawa, daga saɓani irin na harshe da haƙori, zuwa cin zarafi a tsakanin ma’aurata da tauye haƙƙoƙin juna ko kuma rashin samun kulawa, zargi, kishi, da munafurcin abokan zama ko gazawar iyaye.

Wasu batutuwa da suka ja hankalin ‘yan Nijeriya a ‘yan makonnin nan game da sha’anin auratayya, sun haɗa da matsalar cin zarafi da ya shafi duka, zagi, wulaƙantarwa, da aibatawa da ake zargin wasu mazaje na yi wa matansu na aure, wanda wani lokaci har ya kan kai ga sanadin rasa rai. Ban da rahotannin da ake samu na inda wasu mata ke amfani da makami wajen kisan mazajen su na aure ko illata wani sashi na jikin su, bisa dalilai na savani, ƙiyayya ko auren dole, ko ma dai shaye-shaye, da yanzu ke neman zama annoba a tsakanin mata a Arewa.

Wata amarya (ba Musulma ba ce) da aka shirya za a yi auren ta, ranar Asabar 16 ga wannan wata na Afrilu, 2022 da ta gabata, ta fitar da wata sanarwa a shafin ta na sadarwa inda ta sanar da duniya cewa, ta fasa auren ta da za ɗaura da angonta da suka daɗe suna soyayya tare, saboda halayyar yawan zafin rai, cin zarafi na duka da barazanar kisa, tun bayan da ya biya sadakin auren ta. Tana mai cewa, “ba zan iya rayuwa da mutumin da ya ke furta kalaman shi ne zai zama ajalina ko ni in zama ajalinsa ba.”

Wannan ɗaya ce daga cikin dubbannin mata da ke rayuwa cikin ƙunci da azaba, saboda rashin dacewa da mazajen aure nagari masu haƙuri da tsoron Allah. Matsalar da ta zama gama gari ba a arewacin Nijeriya kaɗai ba, har ma da duniya baki ɗaya. Bala’in da masana ke ganin yana da nasaba da matsin tattalin arziki, rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, shaye-shaye, da yawan zafin rai, musamman a ‘yan shekarun baya bayan nan, da matsaloli iri-iri suka dabaibaye duniya.

Ba da jimawa ba ne, wata fitacciyar mawaƙiyar waƙoƙin Kirista, Osinachi Nwachukwu ta rasa ranta a dalilin wata cutar kansa mai kama maƙogwaro, ko da yake ‘yan uwan mawaƙiyar sun ƙi amincewa da wannan dalilin bisa zargin da su ke yi wa mijin matar, Peter Nwachukwu cewa, ta kamu da rashin lafiyar ne a dalilin duka da cin zarafin da mijin nata ya riƙa yi mata tsawon lokaci, wanda kuma ta ke ɓoyewa danginta da mutanen majami’ar da ta ke zuwa, saboda tunanin bai dace ta tona asirin auren ta ba.

Wannan mummunan labari shi ma ya ja hankalin ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin mata da shugabannin Kirista da dama a Nijeriya, duk da kasancewar ba a tabbatar da zargin da ake yi wa mijin marigayiyar da ke tsare a hannun hukuma ba. Amma matsalar ta sake bankaɗo wasu damuwoyi irin wannan da aka daɗe ana binne su, a tsakanin iyaye, da malamai, a masallatai da coci-coci, inda akasari ake ba da haƙuri a nemi ma’aurata su je gida su sasanta, don kar auren ya lalace. Duk kuwa da azabar da a mafi akasari matar ko mijin a wasu lokuta ke fuskanta, a zamantakewar auren.

Sau da dama iyaye, magabata ko malaman addini sukan ba da shawarar ma’aurata su yi haƙuri su ci gaba da zama tare ne, bisa la’akari da yawan ’ya’yan da suka haifa, ko daɗewar su cikin auren da kuma kare kima ko mutuncin iyayen su da nasu, da kuma a wasu lokuta kaucewa shiga fitinar zawarci, da tsoron ɗaukar ƙarin nauyi daga ɓangaren ‘yan uwa da iyaye. Ko da ya ke sakin aure halak ne a koyarwar addinin Musulunci, (amma abin ƙi da ba a son aukuwarsa) da kuma dokokin Nijeriya.

Aure da ake haɗa shi cikin soyayya da kyakkyawan zaton za a yi zama na jin daɗi da faranta ran juna, idan ba a yi dace ba yana zama tarkon mutuwa, ko da kuwa a farkon sa so da ƙauna ne sanadin ƙulla shi. Wani lokaci savanin na samun asali ne daga yadda tun farko aka gino soyayyar da kuma tasirin wasu abubuwa da suke da muhimmanci a rayuwar aure, kamar tarbiyya, ilimi, iyaye nagari da samu ko rashin wadatar abin duniya.

A lokacin da ma’aurata suka fara saurin hasala da faɗawa juna baƙaƙen maganganu, gori ko kalamai na ƙasƙanci, da amfani da ƙarfin iko fiye da yadda sharuɗɗan aure da addini suka gindaya, a kan samu raguwar yarda, soyayya da haƙurin da ake nuna wa juna a farko. Saboda rashin tausayi, ƙuntatawa, zargi, wulaƙanci da cin zarafi da ya kunno kai, cikin wannan iyalin. A irin wannan yanayi ne idan ba Allah ne ya kiyaye aka samu nasarar shawo kan matsalar da wuri ba, ake samun lalacewar zamantakewa, da komawa zaman doya da manja. Ko da kuwa ɗaya daga cikin ma’auratan yana ƙoƙarin ganin mutanen waje ba su fahimci halin da ake ciki ba, kuma igiyar auren ba ta tsinke gaba ɗaya ba.

Kamar yadda malaman addini da ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin ɗan Adam suke ta ƙoƙarin faɗakarwa kan haƙƙoƙin zamantakewar aure, buƙatar kyautatawa juna, kiyaye dokokin zaman tare da muhimmancin nuna kulawa da soyayya. Haka ma a ɓangaren shari’a akwai dokoki da aka tanade su waɗanda kuma ake kafa hujja da su wajen bin kadin wani da aka zalunta ko yake da ƙorafi kan abokin zamansa na aure, don a daidaita tsakani ko kuma a ƙwato wa wani haƙƙinsa ƙarƙashin doka, wani lokaci in ta kama ma a raba auren baki ɗaya.

Jihohin Nijeriya da dama sun kafa dokoki da za su riƙa kula da haƙƙoƙin iyali, kamar mata da yara, amma ana samun ƙorafe-ƙorafe daga wasu masana shari’a da ke kokawa kan rashin ingancin wasu dokokin, da yadda za a yi amfani da su su yi tasiri ga hukuncin da ake so a yi don a samar da adalci.

Dokar gwamnatin Jihar Legas game da cin zarafin juna a tsakanin ma’aurata, sakin layi na (g) ta yi bayani ƙarara dangane da abin da cin zarafi a zaman aure ke nufi, inda dokar ta yi nuni da cewa, cutarwa na jiki da ya shafi yi wa wani lahani, ta hanyar duka ko amfani da makami, cutarwa ta hanyar jima’i, amfani da mugunta a lokacin saduwar aure, saɓanin cutarwa ta hanyar fyaɗe, tilastawa a wajen saduwar aure, hana abinci, wulaƙantarwa, zagi da aibatawa, tauye haƙƙi a kan abin da ya shafi kuɗi ko kasuwanci, hana damar neman ilimi, barazana da tsoratarwa, yawan bibiyar abokin zama da bin ƙwaƙƙwafi, amfani da guba wajen cutarwa, lalata wata kadara ko dukiya, shiga muhallin da ɗaya ya ke ba da izini ba, musamman idan ma’auratan ba a waje ɗaya suke zaune ba, ko nuna wata halayya da za ta iya zubar da mutuncin abokin zama a idon wasu, da jefa rayuwarsa da lafiyarsa cikin haɗari, da hana wa abokin zama walwala ta kowacce fuska.

Waɗannan su ne dalilan da za su iya sa a hukunta wani abokin zama da laifin cin zarafin ɗan uwansa da suke zaman aure. Kuma kamar yadda masana shari’a suka bayyana, doka ta tanadi tarar Naira dubu 50 zuwa dubu 100 ko ɗaurin watanni 6 zuwa shekara ɗaya a gidan yari. Hukuncin da ake jimawa ba a yanke shi ba, saboda ba kasafai matan da aka ci zarafin su a gidan aure ko maza ke kai ƙara kan abin da ya faru ga hukuma ba, ko kuma jurewa matakan shari’a a kotu ba. Kamar yadda wata lauya mai zaman kanta, Barista Mariya Shittu ke faɗa cewa, sau da dama sai ka dage ka bada shawarar abin da ya kamata sai matan su ƙi yarda. Ko kuma idan sun amince an shigar da ƙara sai daga baya su zame su ce sun yafe ko kuma sun daidaita.Wasu ma sai su koma gidan su cigaba da zama, sun bar lauya yana can kotu yana ta haƙilo. Ko kuma a basu shawarar rabuwa da auren idan cin zarafin ya yi yawa don kar ya kai ga sun shiga wani hali ko a rasa rai, amma sam sai su sace wa lauyoyin su gwiwa.

Wani bincike da aka gudanar game da yawaitar saki da cin zarafi a gidan aure a Nijeriya ya yi nuni da cewa, mafi yawan ƙorafin da aka fi samu shi ne na zarge-zargen cin zarafi, zagi da aibatawa wanda ya kai kimanin kashi 52 da ɗigo 3 cikin ɗari. Sai kuma na rashin kulawa da tauye haƙƙi da ya kai kimanin kashi 30 cikin ɗari.

Akwai kuma cutarwa ta jikkata ko lahani a jiki, da ya kai kashi 25 cikin ɗari, yayin da ƙorafin barazanar kisa ya kai adadin kashi 10 da ɗigo 8 cikin ɗari. Sai kuma tilastawa wajen jima’i da ya kai har kashi 14 da ɗigo 2. Wannan adadi ya haɗa har da maza da su ma ake samun kaso mai yawa na waɗanda ke ƙorafin matan su na cutar da su a zaman aure.

Illar da waɗannan halaye na mugunta da cin zarafi ke haifar wa ba ta tsaya kan wanda aka zalunta ba, har ma da yaran da suke tsakanin ma’auratan da ke samun rashin jituwa. Wata mai bincike kan sha’anin zamantakewar iyali Aisha Morohunfola ta bayyana cewa, rikicin iyaye da muzgunawar da ɗaya ya ke yi wa ɗaya abokin zaman yana sa yara su zama koma baya a makaranta ko su faɗa shaye-shaye da yawan zafin rai, kuma su ma idan sun girma suna iya cutar da nasu abokan zaman saboda yadda suka girma suka ga yadda nasu iyayen suke yi.

A matsayina na magidanci mai iyali, na sani zaman tare cikin gidan aure na bulatar haƙuri, tausayawa da kuma kyautatawa ta hanyar nuna wa juna so da ƙauna. Bai kamata ma’auratan da suka haɗu ƙarƙashin inuwar so da ƙauna, da amincewar iyaye, su zama musiba da jarabta ga junan su ba. Babu abin da ya fi zaman lafiya da soyayya daɗi a zamantakewar aure ba.

Lallai ne hukumomi su sa ido wajen faɗakar da iyalai, musamman sabbin ma’aurata tare da samar da wani tsari da zai riƙa kula da ƙorafe-ƙorafe ma’aurata ko abokan zama, ta yadda za a riƙa ƙoƙarin shawo kan matsalolin da ke damun iyali, kafin ya kai ga wani ya cutar da wani, ballantana har a kai ga asarar rai. Kuma lallai ya zama ana amfani da dokokin da suka kamata wajen hukunta waɗanda ke da hannu a yi wa wani abokin zama mugunta ko tauye haƙƙi na ƙeta da zalunci, saboda ƙiyayya ko rashin yarda. 

Allah ya sa mu fi aarfin zukatanmu, kuma ya nufe mu da kyautatawa abokan zamanmu.