Tashin gwauron zabin kayan masarufi a Nijeriya

Magidanta a mafi yawan jihohin Nijeriya na cigaba da ɗanɗana kuɗarsu sakamakon matsananciyar tsadar kayan abinci a kasuwannin ƙasar. Wannan kuwa na zuwa ne daidai lokacin da har yanzu al’umma ke fama da wahalar ƙarancin man fetur da kuma tsadarsa.

Mutane suna ta bayyana takaici kan wannan yanayi da aka samu kai a ciki, inda batun ya zama abin tattaunawa a zauruka da dama na shafukan sada zumunta.

Tuni dai farashin kayan masarufi dama sauran kayayyakin amfanin yau da kullum ya yi tashin goron zabi abin da ya sa jama’a da dama suka shiga cikin ƙuncin rayuwa.

A yanzu haka rahotanni sun nuna cewa akwai mutanen da abin da za su kai bakinsu na salati ma a kullum na matuƙar yi musu wahala.

Masana dai na danganta yanayin da aka shiga yanzu a Nijeriya da wasu abubuwa da suka haɗa da;

  • Ƙarin wutar lantarki da ƙarancin man fetur
  • Dokokin da gwamnati ke yi a kan kuɗi a baya-bayan nan.
  • Tsadar takin zamani
  • Ƙarin Haraji

Waɗannan abubuwa da aka lissafo su ake dangantawa da wasu daga cikin abubuwa da suka haddasa tsadar rayuwa da ma tashin farashin kayayyaki a Nijeriya.

To sai dai kuma a nata ɓangaren gwamnatin Nijeriyar ta bayar da bayanai a kan abubuwan da ta ke gani sun haddasa tsadar rayuwa da kuma tashin farashin kayayyaki.

Batun taki: Karayar tattalin arziki da annobar cutar Korona ta jawo ga ƙasashe na nesa da kusa ya shafi shigo da ma’adinai da ake amfani da su wajen sarrafa taki.

Hakan ya sa taki ya yi tsada a noma har zuwa yanzu, ta yadda waɗansu sun noma shinkafa sun rasa takin saka ma ta dole ta sa suka sayar wa makiyaya shinkafar.

Kafa masana’antun shinkafa: An samu ci gaba wajen kafa masana’antun sarrafa shinkafa da yawa a Nijeriya. Kamar a Kano akwai wajen 18 wanda kowanne a ciki yana sarrafa shinkafa daga tan 180 zuwa 400 a kowace rana. Suna ɗaukar ma’aikata da ba su gaza 200 ba.

Ƙarin farashin man fetur da na hasken wutar lantarkin da aka yi a Nijeriya sun sake jefa ’yan ƙasar a mawuyacin hali.

Batun ƙarin farashin man fetur ma da aka daɗe ana fakewa da shi a matsayin sanadin tashin kayan masarufi, shi ma ba a samu faruwarsa ba a tsawon shekaru,  sai dai a yanzu da aka shiga cikin ƙarancinsa. Hasali ma, an ɗan samun raguwar farashin har karo biyu a baya-bayan nan kamar yadda gwamnati ta ayyana, duk da hakan bai sa an ga raguwar farashin komai ba. Toh, ashe kenan ba daga nan matsalar hauhawar farashin kayan masarufi ta taso ba a yanzu.

A baya dai an sha dambarwa kan batun farashin dala, inda aka samu kusan komai a faɗin ƙasar nan sai da farashinsa ya tashi kuma duk aka jingina lamarin da tashin farashin dalar Amurka. Yanzu haka a iya cewa tuni an wuce wannan wuri, domin mutane sun fahimci cewa ba komai ne farahin dala ya kan shafa ba, masu kaya ne kawai ke sha’aninsu wato dai galibi batun farashin dala ya kamata ya shafi kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙetare kaɗai ne.

To sai dai kuma wasu manoma sun ce idan har aka yi girbin kaka samu amfanin gona to akwai yiwuwar cewa farashin kayan abinci zai iya saukowa.

Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya ta bayyana yadda kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi a watan Disambar da ya gabata, irinsa na farko a cikin wata takwas. Hukumar ta ce tashin farashin ya zarta kashi 15.

Simon Harry, Shugaban hukumar ta ƙididdiga ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a Abuja. Ya ce, abubuwan da suka fi tashi sun haɗa da gas na girki, Masara, kuɗin hayar gidaje, da dai sauransu.

Sauran abubuwan da farashinsu ya tashi sun haɗa da tufanin sakawa da takalma.
Shugaban ya ƙara da cewa, gabanin tashin farahin na Disamba sai da aka yi wata takwas farashin kayan masarufi na sauka a ƙasar ta Nijeriya.

Jihar Ebonyi ita ce ta fi fuskantar tashin farashin kayayyaki a jihohin ƙasar ta Nijeriya, yayin da jihar Kwara kuma ta fuskanci ƙarancin tashin farashin kayayyaki.

Jihar Kogi kuma ita kuma ita ce ta fi tsadar abinci a watan na Disamba, yayin da jihar Edo kuma ta fi arahar abinci a lokacin, a cewar rahoton.

Idan kamfanoni ne ke da alhakin saka farashin da suka ga dama, lallai ya kamata mahukunta su bincika lamarin domin su yi wani abu. Domin su ne aka ɗora wa alhakin kula da haƙƙoƙin al’ummar da suka damƙa amana a hannunsu.

Idan kuma ’yan kasuwa ne ke yin gaban kansu, to lallai su ji tsoron Allah su sa tausayi a ransu, su kuma ji tsoron fushin Ubangiji akan dukiyar da suke tarawa. Su tuna akwai ibtila’i kala-kala (kamar gobara da sata da hatsarin mota da ma karyewar dukiya) waɗanda ubangiji ka iya jarabtarsu da shi, tare da kuma cire albarka da lalacewar a dukiyar da suke tarawa ta irin wannan salo na cin ƙazamar riba.

Da wannan ne Blueprint Manhaja ke kira ga dukkan wani mai hannu a cikin tsaurara wa al’umma da ƙauntata masu a kowanne irin yanayi, kada ya zargi kowa idan ya ga sakamakon abin da ya ke yi ya juyo kansa, akasari kuma irin wannan sakamako na fushin Ubangiji ya kan iya shafar kowa da kowa.