Ko za a iya fille wuyan Buba Galadima?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Me ya sa za a fille wa mutum kai in ba da laifin da shari’a ta tabbatar da shi ba. To in ba haka ba, a bar wa kowa kansa a kan wuyarsa ya yi iya wa’adin zamansa a duniya. A nan ina son tsokaci ne kan alwashin da shaharerren ɗan siyasar hamayya a Nijeriya, Injiniya Buba Galadima ya yi cewa matuƙar shugaba Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓe to a fille ma sa kai. Biyo bayan sanya hannu sai wasu musamman marubutan yanar gizo su ka riƙa tambaya shin wai yaushe za a yi taron fille wuyar Buba Galadima?

Sam ban bar maganar a matsayin hirar teburin mai shayi ba, na bugawa Buba Galadima wuya don jin matsayin wuyarsa a yanzu. Kamar yanda na yi tsammani ba da wata inda-inda ba Galadima ya ce ba wanda ya isa ya taɓa wuyarsa kuma duk mai son a ɗauki wani mataki sai ya nufi kotu da hujjojin sa.

Haka nan ya qara da cewa, ai lokacin da ya yi maganar tun farko an kai ƙudurin dokar da majalisa ta amince da ita ga shugaba Buhari amma bayan cika wata ɗaya sai ya ƙi amincewa da dokar ya turo ta majalisa da buƙatar a yi ma ta gyare-gyare, ciki kuwa har da cire batun zaɓen ’yan takarar jam’iyya ta hanyar ’yar tinke. Bayan haka ma Galadima ya ce, ko a yanzu shugaban ba da zuciya ɗaya ya sanya hannun ba, sai da ya samu gagarumin matsin lamba da kuma hakan barazana ce gaba ɗaya ga babban zaɓen 2023. A tawilin ɗan siyasar mai hamayya ai ko a yanzu shugaban bai sanya hannun baki alaikum ba sai da ya buƙaci a sake gyara wani sashe na 84 a dokar da ke hana masu riƙe da muƙaman siyasa zaɓen ’yan takara ko tsayawa takara sai dai in sun yi murabus. Bai tsaya nan ba sai da ya nuna fargaba cewa a ƙarshe ma za a iya samun dokar ba ta ƙunshe da duk muhimman abubuwan da za a ce za su taimaka a yaqi maguɗi a zaɓe.

A nan ko ma me za a ce shugaba Buhari ya sanya hannu kan wannan doka bayan dogon jeka-ka-dawo da ya fara jefa ayar tambayar ko shugaban ya manta da matsayar sa ta a yi zavien gaskiya da faɗi-tashin da ya riƙa yi da taimakon talakawa ya riƙa takara har sau 4 a tsawon shekaru 12 kafin Allah ya ba shi nasara. Kazalika har an fara zargin ’yan majalisa masu gani-kashenin shugaban na neman hanyar dabara ce ta tsawaita mulkin shugaban ta hanyar zama ba dokar zaɓe, don haka kamar ba zai yiwu a bisa doka a gudanar da babban zaɓen ba.

Ba za a iya kwatanta kowane ɗan takarar shugaban Nijeriya da tsarin shugaba Buhari ba, don shi ne bai samu nasara ba sau uku kuma a kowanne ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen har kotun ƙarshe ta daga ke sai Allah ya isa. Zan tuna a 2007 lokacin da marigayi shugaba Umaru ’Yar’adua ya lashe zaɓe ko hukumar zaɓe ta Maurice Iwu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe ya yi galabar kan Buhari; jam’iyyar Buhari ta ANPP a lokacin sai ta nuna ba za ta ƙalubalanci sakamakon a kotu ba.

Hakan bai karyawa shugaba Buhari gwiwa don ya je kotun har sai da a ka samu alƙalai uku na kotun koli su ka rushe zaɓen su ka yanke hukuncin a gudanar da sabon zaɓe a wata 3. A gefe guda wasu alƙalai 3 su ka mara baya ga zaɓen da korar ƙarar Buhari. A nan marigayi babban alƙali Idris Legbo Kutigi ya kori ƙarar da hakan ne ya sa shugaba ’Yar’adua ya cigaba da zama a mulki har Allah ya yi ma sa rasuwa. Ganin irin hakan ne ma marigayin wanda ya aiyana cewa zaɓen da ya kawo shin a da ’yan matsaloli, ya kafa kwamitin gyaran tsarin zaɓe ƙarƙashin tsohon babban alƙali Lawal Uwais wanda ya yi aiki ya fidda shawarar da ta shimfiɗa alƙiblar gyara dokar zaɓe da har yanzu a ke yi ma ta bita.

A lokacin da ya ke karɓar shaidar lashe zaɓe a 2015 daga hannun tsohon shugaban hukumar zaɓe Farfesa Attahiru Jega, shugaba Buhari a lokacin ne ƙuri’ar masu zaɓe ta yi aiki. Wannan ya nuna tabbacin matsayar sa ta cewa zaɓukan da a ka yi gabanin wannan na da matsala don haka kawai buƙatar gyara. Hakanan shugaban a lokacin da yakan ƙalubalanci sakamako a kotu ya taɓa cewa an hana su damar kawo ƙwararru da za su tantance sahihin ƙuri’un da a ka kada. Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar a zaɓen 2019 da ya yi wa PDP takara ya so a ba shi dama shi ma ya kawo ƙwararrun masu aiki da na’ura don tantance ƙuri’un da a ka kada har a ka ayyana shugaba Buhari ya lashe zaɓe. Shi ma bai samu damar ya kawo kwararrun ba. Irin wannan ya ke daɗa barin zargin nan da a ke yi wa ’yan siyasar Nijeriya da zama tamkar karin maganar nan da ke cewa ‘in jifa ya wuce kai na…” kuma a duk lokacin da su ka lashe zaɓe, shi ne zaɓen gaskiya, amma in ba su lashe ba, to an tafka maguɗi.

Shin waye ne ba waye ba? wa ya tsira daga zargi tsakanin jam’iyyar gwamnati, adawa da hukumar zaɓe? Lashe zaɓe kan zama ga jam’iyya ɗaya in ta samu dama. PDP ta share shekaru 16 ta na jan zaren ta a madafun ikon Nijeriya, inda ba zarar ɗan takara ya samu tikitin PDP sai ka gatun kafin ranar zaɓe a na yi ma sa murna har ma da koya ma sa irin jawabin da zai yi bayan lashe zaɓe. Wani ma kan fara naɗa mataimaka tun kafin kafin zaɓen. Yanzu kuma ba mamaki in ka ga ɗan jam’iyyar gwamnati APC ya lashe zaɓe don kamar tarihi ne ya ke maimaita kansa. Masu zaɓe sun riga sun ga kamun ludayin PDP sun ka na jerin jam’iyyun adawa da su ka narke su ka kafa APC gabanin zaɓen 2015. Yayin da ’yan PDP a zamanin shurarsu, su ka cika baki za su yi shekara 60 kan mulki, kwanakin baya wani babban ɗan APC ya ce su sai sun yi shekara 100! Allah ya jiƙan marigayi Dr. Adamu Danmaraya Jos da ya rera waƙa ya na cewa ‘wa ya san gobe ban da Allah, amma in ka sani mu ganka, wa ya san gobe ban da Allah..’

Ba tun yau Buba Galadima ya raba gari da shugaba Buhari ba, tun gabanin zaɓen 2015 da Buharin ya lashe Galadima ya tattara komatsansa ya koma hamayyar cikin gida. Masu ra’ayi irin na wannan Bawan Allah su na da yawa a cikin waɗanda su ka faro tafiyar shugaba Buhari gabanin fara takarar sa a 2003. Gaskiya ko dai ba za a iya cewa kai tsaye akasarin waɗanda ke tare da shugaba Buhari yanzu sabbin fuskoki ne a tarihin siyasarsa ba, ƙalilan ne cikin waɗanda a ka san shi da su a zamanin gwagwarmaya ke tare da shi. Misalin irin waɗannan mutanen da su ka samu manyan mukamai akwai shugaban hukuamr kwastam Hamid Ali, ministan noma Dr. Mahmud Muhammad, ministan ilimi Adamu Adamu da wasu hadimai na fadar Aso Rock irin su Abdullahi Maikano, Yau Darazo da Sarki Abba.

Masu bibiyar lamuran siyasar shugaba Buhari ba su faye mamakin yadda Buba Galadima ya zama cikin manyan masu caccakar shugaban ba, alhali a baya su ne na gaban goshin kare muradunsa aƙalla dai a kafafen labaru. Bugu da ƙari a yau za a sha mamakin ganin ga gwamnatin Buhari ba Buba Galadima, ba Sule Yahaya Hamma, ba Rufa’I Hanga, ba Mike Ahamba, ba Dr.Bashir Kurfi, ba Usman Bugaje, ba Hakeem Baba Ahmed, ba Abdulkarim Daiyabu, ba Lawal Jafar Isa, ba Zakari Ahmed Nguroje, ba injiniya Magaji Muhammad Yaya da kan kwana ba ya barci in ya ji za a yi wa Buhari magudi, ba ba ba ga sunan da daman gaske. Har sai an gudanar da babban bincike za a fahimci dalilan don gano mai gaskiya ko yadda haƙiƙanin abun ya ke, don ruwa ba ya tsami banza.

Daidai lokacin da zan fara wannan rubutu, na ga shugaban hukumar zaɓe Farfesa Mahmud Yakubu ya fito da sabon jadawalin babban zaɓen da zai fara daga na shugaban ƙasa da ’yan majalisar tariya a ranar 25 ga watan Febrerun 2023 sai na gwamnoni da ’yan majalisar jiha ya biyo baya a ranar 11 ga watan Maris na shekarar.

Hukumar ta kwaranye fargabar raɗeraɗin in ba a amince da dokar zaɓe shekara ɗaya gabanin zaɓe za a iya samun matsala. Ka ga yanzu lamarin zaɓe ya kankama don an zuba suga a kunu an zuba gishiri a miya.

Shugabar kwamitin zaɓe ta majalisar wakilai Aisha Jibir Dukku ta ce duk wata buƙatar inganta zaɓe na cikin dokar har da samar da mafita ga yadda za a yi in Allah ya karɓi ran ɗan takara gabanin kammala zaɓe kamar yadda ya faru a 2015 a Kogi, inda Abubakar Audu ya rasu, amma ba a bada takarar ga mataimakin takararsa ba, Mr. Abiodum James Falake, da hakan ya sa canko gwamna mai ci Yahaya Bello. In dai har yanzu ƙuri’a na aiki, sai talakawa su sake daurewa su zaɓi wanda su ka ga ya fi mu su alheri ga tsaron lafiya da dukiyoyinsu.