Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa da shafin Iyali na jaridar al’umma, Manhaja. Ya yanayin sanyi da haƙuri da rayuwa. Allah Ubangiji Ya shiga lamurranmu, Ya kyautata rayuwarmu.
Idan mai karatu bai yi fashin karanta jaridar Blueprint Manhaja ta makon da ya gabata ba, yana da masaniya kan darasin da muka soma a satin baya, wanda muka yi alƙawarin kawo ci gabansa a wannan mako.
Ga waɗanda suka yi fashi kuwa, mun soma darasin namu na tasirin zagin malamai ga tarbiyyar ‘ya’ya ne da shimfiɗa kan ummul khaba’isin samuwar rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar musulmai, wanda ya zama ƙashin bayan duk wata fitina da ke hudu kai a tsakanin musulmai ciki har da zagin malamai.
Darasin na makon jiya bai gushe ba har sai da ya kawo asalin ƙarfi da Musulunci ya samu a baya da kuma tasirin aƙida a rugujewar haɗin kai na al’ummar musulmai da kuma yadda ta yi sanadiyyar zaman addinin mafi rauni duk da ɗinbin mabiyan da yake da su.
A wannan makon da yardar mai kowa mai komai, za mu kawo bayanin yadda zagin da ake yi wa malamai yake tasiri ga tarbiyyar ‘ya’yanmu. Kafin nan shin mai zagin malamai ke nufi?
Malamai a kowane addini mutane ne masu daraja da ake kallonsu a matsayin baki na saƙon ubangiji gare su. A addinin Musulunci, darkar malami mai matuƙar girma ce, kamar yadda aka tabbatar cewa, Tirmizi da Abu Dawud sun ruwaito cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda ya bi wata hanya domin neman ilimi, Allah zai sauƙaƙa masa wata hanya zuwa Aljanna. Mala’iku suna shimfiɗa fikafikansu ga mai neman ilimi saboda farin cikinsu da abin da yake yi. Kuma duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa suna neman gafara ga mai neman ilimi, har ma da kifayen da suke cikin teku.
Falalar malami a kan mai ibada tana kama da falalar wata mai cikakken haske a kan sauran taurari a daren cikar wata. Malamai su ne magadan Annabawa. Lalle Annabawa ba su bar zinariya ko azurfa a gado ba; abin da suka bari shi ne ilimi. Saboda haka duk wanda ya samu wannan ilimi, to hakika ya samu rabo mai yawa kuma mai albarka.”
Wannan ke nufin suna isar da saƙon addini ne kamar yadda Allah ya umurta, wanda hakan na nufin a girmamasu, domin duk zamanin da annabi ya gushe to sune za su gaje shi ta fuskar isar da saƙon Allah ga al’ummar.
Haka ma aya a cikin Al’ƙur’ani mai tsarki ta faɗa cewa, “Lallai waɗanda suka fi tsoron Allah daga bayinSa su ne malamai.”
Kamar yadda muka sani, hadisi na fassara Al’ƙur’ani mai tsarki ne a lokuta da dama, haka ma malamai suna sawwaƙa wa al’umma ne fahimtar Al’ƙur’ani da hadisi, wanda a wannan zamani ko na bayansa da babu malamai da tuni addinin Musulunci ya zama tarihi.
A ina za mu koyi karatu, da sanin ma’anar abinda littafi mai tsarki ya ƙunsa da ya wuce fahimtar ƙwaƙwalwarmu? Idan har malamai za su sadaukar da lokacinsu da ƙurciyarsu wurin neman sanin saƙon addini, don su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace, da kuwa ko kaɗan ba su cancanci zagi ba.
Idan mun koma ta ɓangaren al’ada ta malam bahaushe, akwai girmamawa da ke tsakanin babba da yaro, ta yadda ko ba kasan mutum ba, za ka girmama shekarunsa. Don haka ɗaya daga cikin manyan illar zagin malamai akwai kawar da wannan ɗab’ia mai tasiri a addini ta malam bahaushe.
Idan ka zagi malami don kawai ba aƙidarku guda ba, ba tare da la’akari da girman abinda yake karantawa ba, da kuma shekarun wanda yake zagi ba, to tabbas ya bayar da dama ga ‘ya’yansa su rena darajar shekaru. Haakan zai iya ba su damar cin mutuncin duk wanda ya taɓa su ba tare da la’akari da shekarunsa ba.
Kuma yana ɗaya daga cikin manyan illolin da ke tattare da zagin malamai, rugujewar tasirin addini a zukatan ‘ya’yanmu masu tasowa. Ta yaya hakan za ta kasance?
Idan za ka zagi malami ɗan wannan ɓangare, yaranka da na mabiya ɗaya ɓangare su ji yadda ka ke aibata da nuna rashin darajarsa, shi ma wancan ya yi wa naka malamin irin wannan zagin, to duka za ku saka yaranku a tunanin wane ne daidai?
Idan sun kalli naka jawabin sai su ji darajar malamin ta zube, idan sun saurari na ɗaya ɓangaren ma haka. Da wannan ne za su shiga tunanin hanyar da take daidai, shaiɗan zai ta kai su ga ƙaryata duk wani abu da suke faɗa, har ta kai ga kwankwanto kan shi karan kansa addinin na Musulunci wanda za su fara zargin kasancearsa gaskiya.
A duk inda zargin malamai ya ɗarsu ga mabiya addini zai fara kawo tasgaro da yardarsu da imaninsu, hakan zai kai ga buɗe zuciyarsu ga yiwar zaman addinin wata hanyar kasuwanci ko neman suna.
Hakan na nufin zagin malamai ba wai iya ku da malaman zai tsaya ba, zai kai ga taɓa tasirinku ma ga ‘ya’yan naku. Domin Allah ne ya ce a yi maku biyayya, idan kuka haddasa abinda zai iya sa su bar ganin ƙimar malamai, zai yi tasiri kan abinda suka koyar da su, wanda zai kai ga naku girman da suke baku, har su yi tunanin bin hanyar da Yahudawa ke ta yekuwa da sunan ‘yancin ɗan adam.
Don haka yana da kyau mu tuna cewa, malamai ma mutane ne, kamar yadda muke kuskure su ma suna yi, idan kuwa sun yi kure, Musulunci ya fitar da hanyoyin da za a bi don karkato su zuwa ga hanya, wanda a ciki babu zaginsu, ko yaɗasu tare da yi masu raddi a bainar jama’a.
Daga ƙarshe, ina so na luarar da mu cewa, zagin malamai barazana ne ga tarbiyyar ‘ya’yanmu masu tasowa ta fuskoki da dama, mu guje yin hakan matuƙar muna son samarwa ‘ya’yanmu makoma mai kyau ta fuskar rayuwa.
