Daga AISHA ASAS
Narkanwa wato abin da bature ke kira da ‘stetch marks’ wani bayyananen zane ne da ke fita ga fata wanda ke rage ma ta kyawo. Ya kan faru ne ta dalilin buɗewar muhallin da ta fito walau ta sanadiyyar ciki ko ƙara ƙiba.
Kaso mafi rinjaye na mata ba sa son ganin ta a fatar su, hakan kan sa su shiga hanyar neman kawar da ita ko ta halin yaya. Kafin komai ya na da kyau uwar gida ta sani, ba komai ne za a baki ki sanyawa fatar ki ba, domin wasu daga cikin ababen da ake bayarwa don maganin narkanwa su kan cutatar da fata. Don haka uwar gida ta tabbatar da ingancin abin da za ta yi amfani da shi.
Ta ya za ki magance Narkanwa?
1. Zuma za ki haɗa da habbatu sauda, sai kin tabbatar da sun haɗe sai ki shafa a muhalin tsayin awani huɗu zuwa biyar sai a wanke. Za a maimaita hakan gwargwadon hali.
2. Man kaɗanya, man zaitun za ki haɗe guri ɗaya sai ki matsa lemun tsami kaɗan a ciki. Za a shafa a muhalin da narkanwa ta fito.
3. Man hulba tare da man zaitun za ki haɗe ki na shafawa tsayin kwanaki 13.
4. Haka zalika man riɗi tare da man zaitun ya na tasiri matuƙa gurin magance matsalar narkanwa.
