Tinubu a matsayin shugaba da zai jagoranci Nijeriya

An ayyana Bola Tinubu, mai shekara 70 a duniya a matsayin mutumin da ya lashe zaɓen shugaban ƙasan Nijeriya mafi ɗaukar hankali tun bayan mulkin sojoji a shekarar 1999.

Tinubu, wanda ake kallo a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa da ya kawo cigaba a jihar Legas, cibiyar kasuwancin ƙasar, ya yi nasara ne kan babbar jam’iyyar adawa mai fama da ɓaraka da kuma ɗan takara na uku da ke da magoya baya matasa.

A ranar 29 ga watan Mayu, na wannan shekara ta 2023, zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki.

Nijeriya, ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka na fuskantar ƙalubalen da suka haɗa da matsalar tattalin arziki da matsalar tsaro da kuma hauhawar farashin kaya.
Da yawa na fatan Tinubu ya fara aiki a ƙasar ba tare da ɓata lokaci ba.

Mutumin da ya taɓa tserewa gudun hijira a lokacin mulkin sojin Marigayi Sani Abacha, Tinubu ya san darajar ’yanci, shi ya sa yake ɗaukarsa a matsayin abu mai muhimmanci.

Ƙwararre kan gudanarwar tattalin arziki, yana cikin ƙungiyar nan mai rajin kare dumukuraɗiyya da ake kira (NADECO), kuma wannan ne mafarin rikicinsu da Abacha.

Ƙoƙarin irin waɗannan ƙungiyoyin irinsu NADECO da kuma mutuwar Abacha a 1998, suna cikin abubuwan da suka haifar da dawowar dumukuraɗiyya a 1999 ta hanyoyi da dama.

Tinubu yana jin cewa yana da haƙƙin shugabancin Nijeriya.

Mutumin wanda mafiya yawan magoya bayansa ke kira da laƙabinsa na sarautar gargajiya ‘Jagaban’, ya ce, yanzu zai duƙufa fara aikin haɗa kan Nijeriya wata ƙasa da ta samu rabuwar kai ta ɓangaren yankuna da addini, kamar yadda sakamakon zaɓen ƙasar ya nuna.

Amma wannan aikin da ke gabansa ba zai tsorata shi ba, saboda ya yi makamancinsa lokacin da yake gwamnan Legas tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 abin da ya qara haskaka shi ke nan a siyasa.

A lokacin shugabancinsa, Legas ta samu kuɗaɗe masu yawa saboda masu zuba jari na ƙasashen ƙetare.

Ya kuma fito da tsarin sufuri da ya bai wa masu mota damar zuwa inda za su cikin gaggawa, sannan ya rage mummunan cunkoson ababan hawan da ake fama da shi a jihar.

Amma duk da wannan birnin mai mutane miliyan 25 har yanzu bai kai matuƙarsa ba duk da ikirarin cewa sun kai shi haka.

Yawancin manyan ayyukan garin duk sun lalace, abubuwan more rayuwa irinsu ruwa da gidaje suma sun taɓarɓare.

Sai kuma tashar jirgin ƙasa mai amfani da lantarki da aka fara a lokacinsa har yanzu ba a gama ba kusan shekara 20 duk da arzikin da jihar ke samu.

Ana zarginsa da sanya idanu kan abin da jihar ke samun duk da ya bar mulkinta tun 2007.

Dukkan gwamnan da ya gaje shi dole ya zama tamkar ɗalibinsa “ya kuma bi sawunsa.”

Duk wanda ya yi ƙoƙarin fanɗarewa nan da nan sai a yi waje da shi, tare da taimakon mambobin ƙungiyar sufuri da suke da tasirin gaske.

Akwai kuma zarge-zargen da ake masa sai dai ya sha musanta su.

Shekaru biyu baya, Dapo Apara wani akawu a kamfanin Alpha-beta, wani kamfani da Tinubu ke da hannun jari mai yawa ta dalilin abokansa, ya zarge shi da amfani da kamfanin wajen halasta kuɗin haram, da kuɗin bogi da ƙin biyan haraji da sauran zarge-zargen cin hanci da rashawa.

An shigar da Tinubu ƙara duk da cewa shi da Alpha-beta sun musanta zarge-zargen sai dai duka ɓangarorin biyu sun amince su daidaita tsakaninsu a wajen kotu a watan Yunin da ya gabata.

Waɗannan zarge-zarge da aka riƙa yi masa sun sanya abokan takarar Tinubu ganin cewa ba shi ba ne mutumin da ya dace da jagorancin Nijeriya, ƙasar da harkokin cin hanci ke da wurin zama.

A zaɓen da ya gabata, an ga wata motar banki da ta kai kuɗi gidansa da ke Ikoyi a Legas, wanda hakan ya janyo zargin da ake masa na zai sayi ƙuri’a ne lokacin zaɓe, babu dai wani mataki da ya ɗauka na musanta hakan.

“Idan ina da kuɗi, in ina so, zan iya raba wa mutane su baki ɗaya, matuƙar ba quri’unsu na saya ba,” in ji shi

Yana ɗaya daga cikin ’yan siyasar Nijeriya masu kuɗi, sai dai kuma akwai tambaya kan dukiyar tasa.

Tinubu ya riqa fuskantar tambayoyi game da lafiyarsa, abin da ya sa ya wallafa wani hoton bidiyo na minti ɗaya da daƙiƙa takwas wanda a cikinsa yake tuƙa keken atisaye domin nuna wa duniya cewa lafiyarsa ƙalau.

Abokan hamayyarsa sun ce shekaru sun cimmasa inda suka riƙa wallafa wasu hotunan bidiyoyi da ke nuna shi yana magagi a wajen yaƙin neman zaɓe, abin da yake faɗa ba a fiye ganewa ba.

Da yawan ’yan Nijeriya na nuna damuwa kan matsalar rashin lafiya bayan shugaban da aka taɓa yi mai irin wannan matsalar Umaru Musa ’YarAdua da ya rasu yana kan mulki a 2010.

Shi ma Shugaba Buhari da yake mulki ya ɗauki lokaci yana fama da rashin lafiya, abin da ya riqa sanya shi tafiya Turai neman magani akai-akai.

Sai dai mabiyansa na cewa yana da ƙwarewar aiki, kuma shugabanci ba tsere ba ne balle a bar shi a baya.

Yayin yaƙin neman zaɓe, an yi ta samun faɗi-tashi game da wanda za su yi takara tare.

Tinubu wanda Musulmi ne daga kudanci, ya ɗauki tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima daga arewaci a matsayin mataimakinsa.

An riƙa yi wa hakan kallon birgewa da neman janyo Musulman da ke yankin arewacin Nijeriya waɗanda suke da masu zave da yawa a ƙasar.

Hakan ya janyo cece-kuce daga Kiristocin Nijeriya da suka ce hakan ya ci karo da yadda aka saba, na haxa waɗanda ba addinansu ɗaya ba takarar shugabancin Nijeriya.

Ya kare matsayarsa kan cewa ya ɗauke shi ne domin cancanta ba wai domin abin da mutane ke so ba.

Ana masa kallon ‘ubangida’ a siyasar kudu maso yammaci kuma mafi ƙarfin faɗi-a-ji, domin shi ne ke faɗin yadda za a yi da iko tsakanin yaransa.

A 2015, ya bayyana kansa a matsayin “ƙwararren mafarauci” kuma shi ne ke kai “ƙwararru ofis.”

Ƙarfin ikonsa ya kai ga yin gamayyar jam’iyyun ’yan hamayya a 2013 wanda a ƙarshe suka ƙwace iko daga hannun jam’iyya mai mulki ta PDP a 2015, wani abu da bai fiye faruwa ba a mulkin Nijeriya a kayar da shugaba mai mulki.

A lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyarsa, yayin da Tinubu ya nuna buƙatarsa ta tsayawa takarar, ya tunasar da ’yan Nijeriya da bugun ƙirji cewa shi ne ya kawo Shugaba Buhari ga shugabancin Nijeriya, bayan tsohon shugaban sojin ya yi ta ƙoƙarin samun nasara amma yana faɗuwa.

Shi ya sa magoya bayansa da dama ke kallon mataimakin Buhari Yemi Osinbajo a matsayin wanda ya yi butulci, saboda a baya ya yi wa Tinubu kwamishina kuma ya zo yana neman karawa da shi a takarar shugaban Nijeriya.

Da wannan nasara da ya samu akwai matsalolin da ke gabansa waɗanda dole ya yi aiki a kansu da Buhari ya bari bai yi ba.

Misali, matsalar tsaro da rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki ga kuma rabe-raben da ake samu ta ɓangaren ƙabilanci. Ba wani aiki ba ne da ke da wuya, amma aiwatarwar kan zama mai wuya.