Tinubu ya rattaɓa hannu kan tsohon Taken Ƙasa ya zama doka

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanya ya rattaɓa hannu kan Dokar Taken Ƙasa inda a yanzu za a koma amfani da tsohon taken ƙasa wanda Turawan mulkin mallaka suka samar.

Tuni dai wannan al’amari ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan ƙasa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman da Majalusar ta yi a ranar Laraba.

Haka nan, Akoabio ya ce Shugaba Tinubu ba zai yi wa Majalisar jawabi ba illa iyaka ya ƙaddamar da sabon taken na Nijeriya.

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Tinubu ya soke gabatar da jawabin ne kasancewar Ranar Dimokuraɗiyya ta koma 12 ga watan Yuni.

Ga dai yadda tsohon taken ƙasa da Tinubu ya sanya wa hannu yake:

Nigeria, we hail thee,
Our own dear native land,
Though tribe and tongue may differ,
In brotherhood, we stand,
Nigerians all, and proud to serve
Our sovereign Motherland.

Our flag shall be a symbol
That truth and justice reign,
In peace or battle honour’d,
And this we count as gain,
To hand on to our children
A banner without stain.

O God of all creation,
Grant this our one request,
Help us to build a nation
Where no man is oppressed,
And so with peace and plenty
Nigeria may be blessed.