Tsaro: Gwamnan Zamfara ya kama hanyar samar da Rundunar Kare Garuruwa

A matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ke yi na inganta tsaro a faɗin jiharsa, ya kafa wani kwamiti musamman da zai fara aiki don assasa Rundunar Kare Garuruwa, wato “Community Protection Guard” a Turance.

Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook a ranar Laraba.

Ya ce, “Bayan kwashe awanni muna tattaunawa kan harkar tsaro, a yau na ƙaddamar da kwamitin da zai fara aiki don samar da Rundunar Kare Garuruwa (Community Protection Guard).

“Wannan yana daga cikin shirinmu don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Zamfara.

“Babban aikin wannan kwamiti shi ne samar da tsari wanda da shi za a kafa wannan rundunar ta CPG, don mu iya bada kariya ga garuruwanmu bakiɗaya.

“Aiki ne babba, amma da yardar Allah za mu yi nasara.

“Babu gudu, ba ja da baya a ƙudurinmu na kawo ƙarshen ‘yan bindiga. A dalilin haka nake sake nanata cewa ba za mu yi sulhu da maɓarnata ba,” in ji shi.

Gwamna Lawal ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar, Malam Mani Malam Mumini, sai kuma wasu masu ruwa da tsaki a matsayin mambobi.

Sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, kwamitin da aka kafa ɗin zai nazarci matsalolin da aka fuskanta sakamakon ayyukan ‘Yan Sa Kai’ da aka haramta a jihar da zummar bunƙasa dakarun kare garuruwa da za a kafa.