Tsohon minista Dalung ya jagoranci zanga-zanga a Jos

Spread the love

Tsohon minista a gwamnatin da ta shuɗe, Solomon Dalung ya jagoranci zanga-zanga a birnin Jos.

Masu zanga-zangar wanda mafi yawan su matasa ne, sun yi tattaki inda suke waƙoki suna daga abun rubutu da ke nuni da buƙatar su.

Yayin da yake magana, Dalung yace wannan zanga-zanga ba don komai ake yin ta ba sai don a samu shugabanci nagari da kuma neman gwamnati ta sassauta matsin rayuwa da ake fama dashi.

Bayan shi, wasu da dama daga ƙungiyoyin sa kai sun yi magana inda su ma suka buƙaci shugaba Tinubu da ya dage ya yi wani abu a kan matsin rayuwa da yunwa da ake fama dashi.

By ukarofi