Haraji: Kamfanin lantarki na Kaduna ya yanke wutar gidan gwamna a matsayin martani

Spread the love

Kamfanin lantarki na Kaduna ya yanke wutar gidan gwamnatin Jihar Kaduna.

Hakan ya faru ne bayan rufe ofishin Lantarkin da hukumar haraji ta yi a safiyar Juma’a saboda bashin miliyan 600.

Domin mayar da martani, kamfanin ya yanke wutar lantarkin gidan gwamnatin suma saboda bashin biliyan 2.9.

Mai magana da yawun kamfanin, Abdulazeez Salisu ya bayyana kamfanin yayi iya bakin ƙoƙarin shi domin ganin gwamnatin ta yi abunda ya dace kafin a basu gargaɗin yanke wutar tun 21 ga watan Yuli sai sai abun yaci tura.

By ukarofi