Wai me Buhari yake zuwa yi Daura?

Daga RAHAMA ABDULMAJID

Abin mamaki ne matuƙa yadda shugaba Buhari ya mayar da zuwa ƙauyensu yawon salla kamar wani rukuni na biyu a shika-shikan Musulunci.

Ba zuwansa Salla ko ƙauyen ne ke ci min tuwo a kwarya ba, a’a yadda a matsayinsa na tsohon jami’in tsaro ya san tasirin nuna naƙasu ko jarumta na jagora a idon maƙiya, kuma aka sha shi ya warke a kan hakan. Amma sam taurin kai baya bari ya ɗauki darasi har a kan kansa balle waninsa.

A watan Agusta na shekarar 1985, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tafi Hajji a matsayin Amirul Hajji inda ya zamto Shugaban Ƙasa ne riƙe da ƙasa a zamanin da babu isasshen hanyar sadarwa ballantana mutum ya riƙa juya ƙasar daga kan gadonsa. Hasalima, layin waya a bakiɗayan Najeriya lokacin bai wuce dubu 19 ba, kuma da zarar an yi ruwa ko an ɗauke wuta suke ɗauke sabis, sai illa Masha Allahu.

Amma maimakon Shugaba Buhari ya zauna a Dodon Barak ya yi sallarsa cikin riƙe amanar ‘yan ƙasa, haka ya ja mota ya tafi Daura ya bar ƙasa a hannun wasu SMC, ba shugaba ba mataimaki. Ɗaya na sauke farali, ɗaya na ƙauye. A haka IBB ya afka Dodon Barrack ya zarewa COS ido ya ƙwace mulki. Shugaba da mataimaki suka dawo gotai-gotai aka kwashe su aka wurmusa su a gidan maza. Wannan ya yi sanadiyyar sai da muka shekara 13 a hannun sojoji.

Yanzu ana daf da salla yana daf da sauka ya sake fara shirin ƙauye har an fara ɗebe jami’an tsaron ƙasa ana tura su ƙauye don kare shi, shi kaɗai. Kwatsam! an kai musu hari, an raunata wasu su kuma sun kasa kama yan ta’addan.

Ba damuwata an kai wa me karambani hari ba, damuwata ita ce tasirin da irin wannan hari kan yi wa tsaron ƙasa.

  1. Zai ƙara wa ‘yan ta’adda ƙwarin gwiwa
  2. Zai kashe gwiwar yan ƙasa da ke shirin fitowa don kare kansu da kansu.
  3. Zai ƙara zubar da mutuncin jami’an tsaron ƙasa.
  4. Zai ƙara yaɗa labaran rashin tsaro ta inda babu me zuwa zuba jari a ƙasar da shugaban kasa ma ana iya kai masa hari balle wasu masu hannun jari.

Kuma wai duk don zai je ƙauye Sallah da dabbobi ne fa za mu shiga wannan halin tunda in dai don iyalai ne, duk sun kama ɗaki a gidan gwamnati.

Rahama Abdulmajid ta rubuto daga Abuja