Arewa: Idan jifa ya wuce kanka, ya faɗa kan uban kowa!

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

Matuƙar ‘yan Arewa suna kan wannan irin batu da fahimtar, ni in har zan amfana ko kuma in har na samu to kowa ya mutu, ko kuma in har na tsira to kowa ya hallaka, to Arewa za tai ta ganin abin baƙin ciki yau da gobe.

Irin wannan tunanin ne ke sanya wasunmu ke bin azzaluman ‘yan siyasa, saboda in har za su ba su kuɗi, to sauran al’umma su mutu.Har ka ji ana ihu ana cewa “Ruwan da ya dake ka shi ne ruwa”

Irin wannan ne ke sanya ka ga mutane sun haɗa kai da ‘yan ta’adda suna ba su bayanin sirri yadda za a farmaki ƙauye ko a sace jama’a. Idan har za su ba su kuɗi. Ba kwanaki aka kama mata suna jigilar man fetur ga ‘yan ta’adda ba? Wai saboda kuɗi ba? In sun samu kuɗin to kowa ya mutu.

Irin wannan lalataccen tunanin kwata-kwata ya ci karo da ci gaban al’umma, shi ke ƙara wa rashawa, cin hanci, zalunci da sauransu ƙarfi.

Wannan tunanin na daga cikin manyan matsalar Arewa, kuma wallahi ya na ɗaya daga cikin jiga-jigan abun da zai rusa Arewa matuƙar ba su canza ba.

“Idan gemun ɗanuwanka ya kama da wuta, ka shafawa na ka ruwa” SHIRME NE! Ka taimakashi ya kashe, shi ne daidai.
“Ruwan da ya dake ka, shi ne ruwa” GIDADANCI NE”
“Ruwan da ya daki kowa, shi ne ruwa” HANKALI NE

“In jifa ya wuce kan ka, ya faɗa kan Uban kowa” JAHILCI NE DA HAUKA

“In jifa ya wuce kan ka, kar ya faɗa akan kowa”

Mukhtar Sipikin marubuci mai bayyana ra’ayi.