Shin ‘yan ta’adda sun fi ƙarfin jami’an tsaronmu ne?

Daga SALMAN MUKHTAR

A kwanakin baya an kai hare-hare guda biyu da suka ɗauki hankalin mutanen Najeriya, waɗanda sun ƙara fito da asalin ƙarfin ‘yan ta’adda da kuma nuna yatsa ga ƙarfin jami’anmu.

Hari na farko, shi ne wanda aka kai gidan gyaran hali na Kuje (Abuja), inda waɗannan maciya amanar ƙasa su ka yi ta harbe-harbe tare da ɓalle wannan magarƙama, in da rahotanni suka nuna aƙalla kashi 90% na mutanen da ke ciki sun tsere.

A cikin wanda aka nema aka rasa a wannan magarƙama, har da tsohon jami’in ɗan sanda, Abba Kyari, da ake tuhuma da laifin safarar miyagun ƙwayoyi, da tsofaffin gwamnoni guda biyu da aka ɗaure da laifin almundahana da kuɗaɗen jihohinsu, watau gwamnan Taraba, Jolly Nyame, da takwaransa na Filato Joshua Dariye.

Ma fi muni daga cikin harin, shi ne, tserewar duk wasu tsararrun ‘yan Boko Haram da suke cikin gidan, kamar yadda ministan tsaro na ƙasa, Janaral Bashir Magashi, ya shaida wa wata majiyarmu.

Hari na biyu, shi ne wanda aka kai wa tawagar shugaban ƙasa Buhari, duk da jami’an tsaro sun daƙile wannan hari, amma fa hakan na nuna cewa tun da tawagar shugaban ƙasa ba ta tsira ba, to mu talakawa a su wa?

Haqiqa jami’an tsaronmu suna ƙoƙari wajen daƙile hare-haren waɗannan tsinannu, don mun ji a kwana-kwanan nan yadda suka hana faruwar hare-hare da dama a jihar Kano da kuma ƙoƙarin da suke a sauran yankunan da wannan matsala ta tsaro ta addaba.

Amma fa tilas, sai an qara jajircewa, sai gwamnati ta yi kamar tana yi, sai mutane sun ba wa jami’an tsaro haɗin kai, kafin a kawo ƙarshen wannan musiba.

Allah ya ba mu zaman lafiya a ƙasar mu Najeriya.

Salmanu Mukhtar Paris ya rubuto daga Kano