Gaskiya ɗaya ce: Buhari ba shugaban ƙasa ba ne, ministan harkokin ƙasashen wajen Nijeriya ne

Daga LARABI LARABEEN

Idan da Shugaba ne ba zai shirya tafiya cikin abinda ko awa goma sha biyu ba a yi ba da kai wa tawagar masu tsaren lafiyarsa ba. Kuma har an samu asarar rayukan jama’a a cikinsu.

Idan da Shigaba ne ba zai tsallake zuwa wata ƙasar ba cikin abinda bai wuce awa goma sha biyu da kai hari babban gidan gyaran hali na Kuje inda fursunoni kusan 600 suka tsere daga gidan bayan harin da aka kai.

Idan da Shigaba ne ba zai samu sukunin tafiyar ba. Bayan abinda bai kai ko sati guda ba daga dawowarsa daga ƙasar Portugal.

Kai anya wannan shugaba yana da masu ba shi shawara kuwa? Ai ko yawon da yake yi a sararin samaniya ya kamata a ce in akwai masu bashi shawara su sa ya tsagaita saboda tsufansa zaman Jirgin sai ya tambaye shi.

Hakan likitocin da suke kula da lafiyarsa ba sa ba shi shawarar yawan yawo a jirgin kan iya haifar masa da matsala ta ɓangaren lafiyarsa?.

Ina takaici matuka ina kuma Allah wadai da duk wani mara tunani da ya sake mafarkin zabo mana shugaba irin Buhari.

Wannan Yawace-Yawacen da yake yi, aiki ne na ministan harkokin waje, ba n shugaban ƙasa ba ne. Shugaban ƙasa an zaɓe shi ne don ya zauna a ƙasa cikin ofis ya yi wa mutanen ƙasar aikin raya ƙasa da inganta tattalin arzikin ƙasar.

A ƙasashe irinsu Chana da Amurka da Saudiyya da sauran ƙasashen da suka cigaba kai har ma da ƙasashen Afrika masu tasowa, babu wani shugaban ƙasa da zai shirya maka tafiye-tafiye acikin wata guda sau uku. Amma shi Buhari cikin Wata Guda yayi tafiye-tafiye ya kai sau 4 ko 5 duk kuma da kuɗin ƙasarmu Nijeriya. Sannan ya kwaso Iyalansa har da na gidan aure su yi tafiyar kawai don a basu alawus. Wannan wane irin zalunci ne? Wane irin rashin lissafi ne?.

Kuɗin da Buhari yake tafiye-tafiye dasu kaɗai ya isa a ce an yi ayyukan raya ƙasa dasu wanda ko bayan barin mulkinsa za a gani a tuna da shi? Amma yanzu da me zamu tuna Buhari da shi idan ya bar mulki?

‘Yan bindiga?
Satar mutane?
Tsadar Rayuwa?
Yajin aikin ASUU?
Rashin aikin Yi?
Rashin samar da Tsaro?
Rashin samar da Ingantattun hanyoyin sufuri na ƙasa?
Tsadar fetur?
Tsadar Gas?

Ko kuwa da yawan yawace-yawacen da yake yi a sararin samaniya yake so mu tuna da shi?.

Shin daman abinda ya zo yi wa ‘yan ƙasa kenan amma ya dame mu da cewar waɗanda suke kan mulki suna zaluntar mu? Bayan shi ne mafi munin shugaban da ya zalunci ‘yan ƙasarsa tunda ya kasa tsayawa ya zauna a ofis ya gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa na al’ummar da ya yi alƙawarin zai mulke su, zai musu adalci, zai samar musu da tsaro, zai inganta lafiyarsu da tattalin arzikin ƙasar?.

Tun 2003 nake jefa wa Buhari ƙuri’a. Har aringizon ƙuri’a na yi domin Buhari ya samu ya haye a 2003 zuwa 2011. Kafin a fara amfani da ‘Card Reader’. Saboda Buhari nake neman aikin wucin-gadi na aikin zaɓe.

Amma da wannan rashin kulawar zai saka mana? Da wannan rashin tsaron zai saka mana? Da yajin aikin ASUU zai saka mana? Yadda Malamai da ɗaliban Jami’a suka bada gudummawa wajen ganin ya kafa gwamnati musamman farfesoshi da suka zama sune manyan masu ruwa da tsaki wajen gudanar da zaɓen da ya samu damar kada Jonathan.

Ya Allah muna tawassali da kyawawan sunayenka tsarkaka da kuma wannan Watan Zul-Hijja. Ya Allah muna Tawassali da Manzo Sallallahu Alaihi Wassallam ka kawo mana ƙarshen Wannan mulkin na sakaci da rashin ko in kula da halin da ‘yan ƙasa suke ciki a kasarmu Nigeria. Ya Allah kada ka bawa duk wani azzalumi ko wanda bai damu da halin da duk ‘yan ƙasa za su shiga ba irin Buhari mulkin ƙasarmu Nijeriya a zaɓen da yake gabatowa na 2023.

Larabi Larabeen marubuci ne mai bayyana ra’ayi.