Wai wanne ’yanci da daidaito mata suke nema ne?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Duk shekara a kowacce ranar 8 ga Maris, mata a ko’ina a faɗin duniya suke gudanar da bukin Ranar Mata ta Duniya, bukin da aka fara tun daga shekarar 1975 lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince a hukumance a ware wannan rana don tattauna batutuwan da suka shafi mata da ƙalubalen da suke fuskanta a rayuwa.

Gabannin wannan lokacin, mata sun kasance suna bayyana matsalolin su da buƙatunsu ta hanyar ware wata rana domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin daɗi da wata halayya da suke ganin tana takura wa ’yancin su ko tauye musu wata dama da suke ganin suna da ita, amma maza ba sa amincewa su sake musu.

Mata a Amurka sun ware ranar 28 ga watan Fabarairu na shekarar 1909 sun gudanar da wata zanga-zanga, domin tunawa da cika shekara guda da mata masu aikin ɗinki barguna suka yi a birnin New York saboda nuna rashin jin daɗi da yanayin aikin su, wanda suke cewa ana matuƙar takura musu.

Haka ma aka yi a ƙasar Rasha a shekara ta 1917 inda a ranar 23 ga watan Fabarairu mata a ƙasar suka gudanar da zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar biredi, ranar da aka ce daidai da ranar 8 ga watan Maris na kalandar Giregori. Don haka aka amince kan amfani da ranar 8 ga watan Maris, a matsayin Ranar Mata da a ko’ina a faɗin duniya za a riƙa raya ta, da nufin faɗakar da jama’a wasu muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar mata.

Don haka a hukumance za a iya cewa, an fara bukin Ranar Mata ne a duniya rana ɗaya a tare, tun daga shekarar 1977 bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana ware wannan rana ta 8 ga watan Maris. Ko da ya ke tarihi ya nuna tun a 1848 mata suka fara haɗuwa don kare muradun su da bayyana rashin jin daɗin su da wani tsari na rayuwa, inda aka ce a shekarar ne wasu matan turawa ‘yan ƙasar Amurka, Elizabeth Cardy Stanton da Lucretia Mott, suka jagoranci shirya wani babban taron mata na yaƙi da bauta a Amurka. 

A kowacce shekara kuma ana ɗaukar wani muhimmin batu da za a mayar da hankali a kansa, a matsayin jigon saƙon da ake so a fahimtar da duniya a kai, bisa la’akari da abubuwan da suka fi ɗaukar hankalin duniya a lokacin. Kamar yadda a bana aka ɗauki batun, samar da daidaito tsakanin maza da mata a yau, zai kawo ɗorewar kyakkyawar rayuwa a gobe!

A bikin wannan rana na bana, kirarin a daina nunawa mata wariya, shi ne ya mamaye ko ina, a kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta. An ɗauki hotunan mata sun giciya hannaye su, alamar da ke nuna suna goyon bayan kiran ‘a daina nuna wa mata wariya!’

Wannan take babu shakka ya ja hankalina sosai, kuma na tabbata ba ni kaɗai ba ne har da wasu jama’a da dama, musamman daga vangaren maza, waɗanda matan ke zargin sun mamaye komai sun hana su rawar gaban hantsi.

Ba tare da mun waiwayi rayuwar mata a wasu ƙasashen ba, a Nijeriya dai za mu ce sambarka ne da irin ’yanci da walwalar da mata ke ciki, ba tare da wata ƙuntata ko cin zarafi na gama gari ba, da zai nuna rashin ’yanci ko wariya ga jinsin mata ba. Ko da ya ke wannan ba yana nufin a ɗaiɗaiku ba a samun ƙorafe-ƙorafe na tauye haƙƙin mata ko cin zarafi ta dalilin zamantakewar aure ko al’ada ba. Amma a Nijeriyance za mu iya cewa rayuwar mata na gudana ne kamar ta kowanne ɗan ƙasa, ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasa.

Mata na ’yanci da damar neman ilimi, neman sana’a, neman kuɗi, neman muƙamin siyasa, neman wani matsayi a wajen aiki ko a makaranta, da sauran duk wata hidima ko fafutuka ta zaman rayuwa, babu inda doka ta hana. A wasu wuraren ma matan sun fi yawa har sun ninka maza samun wata damar saboda yawan su, kamar a wajen karatu ko wajen aiki.

A makarantu da dama za ka tarar fiye da rabin ɗaliban da ke wani aji ko nazarin wani Kwas a jami’a duk mata ne. Tun daga firamare har jami’a, yanzu haka mata sun kere maza a yawa. Haka ko da a wurin neman aiki ne, mata sun fi saurin samun aiki fiye da maza, kuma hatta a matakin shugabanci sai ka tarar mata sun fi yawa, a ma’aikatu da dama.

A vangaren neman kuɗi da kasuwanci ma, inda ake ganin kamar harka ce ta zallar maza to, yanzu nan ma mata ne ke cin karen su babu babbaka, domin kuwa akasari a wasu wuraren su ne masu jari mai yawa, su ne masu ba da sarin kaya, ko sayen kayan aiki da sauran su. Hatta a wajen cin kasuwa sai ka yi mamakin yadda mata ke gogayya da maza. Har ma a wasu garuruwan akwai kasuwannin da ake ce wa Kasuwar Mata, saboda cincirindon mata masu saye da sayarwa, sun doke tasirin maza, sai dai tsiraru.

Duk wannan na faruwa ne, saboda yawan ƙorafi da nuna ana yi musu wariya, ko ba a yin yadda zai dace da bukatun su da sauran dalilai, don haka sai a yi ta ba su fifiko da ba su dama fiye da maza, don a ƙarfafa musu gwiwa kuma a kashe bakin tsaka!

Wurin da za a iya cewa har kawo yanzu mata ba su mamaye shi ba, shi ne fagen siyasa! Nan ɗin ma suna cewa, addini da al’adu su ne suke yi musu tarnaƙi, da kuma uwa uba rashin kuɗaɗe a hannunsu ko rashin gogewa a harkar. Shi ya sa suke kukan ba a basu dama sosai a sha’anin tafiyar da mulki da siyasa.

Wannan ce ta sa idan lokacin siyasa ya gabato, don jawo hankalin mata masu ra’ayin siyasa sai wasu jam’iyyu su riƙa ba su takardun neman tsayawa takara kyauta, ko kuma a ware wasu muƙamai ko kujerun majalisa a ce sai mata ne za su nema, don dai kar su yi ƙorafin ana yi babu su.

Ko a ranar Laraba ta makon da ya gabata 2 ga watan Maris, sai da dandazon ƙungiyoyin mata daga sassan Nijeriya suka yi wata zanga zangar lumana a gaban Majalisar Ƙasa suna masu bayyana rashin jin daɗin su da wasu matakai da ’Yan majalisar suka ɗauka game da wasu buƙatun da matan suka shigar don ganin an yi kwaskwarima a kai, a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa, buƙatun da rahotanni suka ce sun shafi dokoki 5, da Majalisar Ƙasa ta yi nazari a kansu.

Daga ciki akwai buƙatar da matan suka shigar ta neman a ƙara ware musu kashi 30 cikin ɗari na muƙaman da gwamnati ta ke naɗawa, a maimakon kashi 20 cikin ɗari da dokar ƙasa ta amince da shi. Wannan ya jawo wa ’yan majalisar ƙasa tofin Allah wadai, da zargin rashin kishin cigaban mata, da nuna wariya a siyasance, daga ƙungiyoyin mata da wasu manazarta masu rajin kare haƙƙoƙin ɗan Adam. 

Ba manufar wannan rubutu ne, dakushe ƙoƙarin da mata ke yi na nema wa kansu ƙarin ’yanci da walwala ba, ko kuma musanta cewa, mata na fuskantar wasu matsaloli na rayuwa da ya kamata a ɗauki matakin magance su a gwamnatance ko a al’ummance ba. Babu shakka na sani wasu koke koken da mata ke yi musamman waɗanda suka shafi zamantakewa da al’adu gaskiya ne. 

Ana samun wasu mazaje da ke cin zarafin matan su, danne musu haƙƙoƙin su, wulaƙanta su da ma ƙasƙantar da su, saboda kasancewar su mata. Wasu ƙabilu na da wasu al’adu da ke tozarta jinsin mace da fifita ɗa namiji a kan rayuwar ’ya mace. Kai ka ce har yanzu muna rayuwa ne a zamanin dauri. 

A irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe muna iya cewa, lallai dole mata su ɗaga muryoyinsu kuma su ƙara dagewa wajen amfani da ilimin su da gogewar su, don kawo ƙarshen cin zali da tauye haƙƙoƙin su da wasu maza ke yi. Yayin da a gefe guda kuma zan ce in ban da dokin mai baki ya fi gudu da sai in tambayi, wai shin wanne ’yanci da daidaito mata suke nema ne, ban da mamayar da suka yi wa maza! 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *