Wani Bature yayi tattaki daga Landan zuwa Makka da ƙafa

Wani mutum mai shekaru 52, Adam Muhammed, ya yanke shawarar yin tattaki daga birnin Landan zuwa Makka na Saudiyya da ƙafa. Ya fara tafiyar ne a watan Agustan 2021.

Tsawon watanni da fara tafiyar, ya kan rubuta komai da ke tafiya ta yanar gizo, inda mabiyansa suke taya shi murna da ƙara masa ƙarfin gwiwa.

Mutanen da suka san inda ya sauka a kowane lokaci sukan ba shi makwanci, su ciyar da shi, kuma su taimaka masa wajen ci gaba da tafiyarsa, in ji rahoton TRT Word.

Ya samu shiga ta ƙasashen Netherlands, Jamus, Czech, kuma a halin yanzu yana birnin Istanbul a ƙasar Turkiyya.

Adam ya ƙuduri burinsa na zuwa Makka da ƙafa ne a watan Yuli. Yana shirin bi ta Syria da Jordan. Hotunansa da aka yaɗa a manhajar Instagram sun nuna shi yana daga hannu a kyamara yayin da yake sakin murmushi. Mutane da dama sun mayar da martani kan wannan kyakkyawan niyya.