Wani mai gadi ya rasa ranshi yayin raba faɗa

Rundunar yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cewa wani mai gadi mai suna Yusuf Akadogo, ya rasa ransa yayin da yake raba faɗa tsakanin wani ɗan achaɓa da wani mutum.

Mai magana da yawun yan sandan na Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya sanar da hakan a yau talata.

Ya ƙara da cewa ɗan achaɓar dai ya gudu, har yanzu ana neman shi.Ya kuma ƙara da cewa an yi hanzarin kai Mai gadin asibitin jami’ar jihar Legas, saidai a can ne rai ya yi halinsa.