Xi ya yi kira da a inganta mu’amalar al’ummomin Sin da ƙasashen Larabawa mai makoma ta bai-ɗaya

Daga CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kasashen Sin da na Larabawa, da su ci gaba da raya dangantakar abokantakarsu, da inganta mu’amala tsakanin al’ummomin Sin da kasashen Larabawa mai makomar bai daya, yayin da yake jawabi jiya Jumma’a a taron shugabannin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na farko.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shirye kasar Sin take ta zurfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare da kasashen Larabawa, da nuna goyon baya ga juna, wajen kiyaye ikon mallaki, da cikakkun yankunan kasa, da kare martabar kasa.

Yana mai cewa, ya kamata bangarorin biyu su kiyaye ka’idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe. da aiwatar da ra’ayi na gaskiya tsakanin bangarori daban-daban, da kare ‘yanci da muradun kasashe masu tasowa.

Xi ya bayyana cewa, ya kamata a hada kai wajen nuna adawa da nuna kyama ga addinin Islama, da aiwatar da hadin gwiwa wajen kawar da tsattsauran ra’ayi, da yin watsi da danganta ta’addanci da wata kabila ko addini.

Ya kara da cewa, ya kamata a ba da shawarar dabi’ar bil-Adama ta bai daya ta zaman lafiya, da ci gaba, da daidaito, da adalci, da demokuradiyya da ‘yanci.

Shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta yi aiki tare da kasashen Larabawa, don ciyar da wasu manyan tsare-tsare guda takwas na hadin gwiwa gaba, a fannonin da suka hada da tallafin raya kasa, da samar da isashen abinci, da kiwon lafiyar jama’a, da kirkire-kirkire ba tare da gurbata muhalli ba, da samar da isashen makamashi, da tattaunawa tsakanin mabambantan al’adu, da ci gaban matasa, da tsaro da kuma zaman lafiya.

Mai fassara: Ibrahim