Ya kamata Tinubu ya yi taka-tsan-tsan da tsoma baki a siyasar Kano -Buba Galadima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani jigo a Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan wajen tsoma baki a siyasar jihar Kano.

Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.

Ya ce, “Ya kamata gwamnatin tarayya da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu su yi taka-tsan-tsan da shiga siyasar Kano. Zai lalata shugabancinsa.”

Ya yi Allah wadai da goyon bayan da gwamnatin tarayya ke baiwa wata ƙungiya a siyasar Kano, yana mai cewa bai kamata hukumomin tarayya su karkata kan sha’anin sarautar Kano ba.

Shugaban NNPP ya jaddada tsayin daka da jajircewar mutanen Kano.

Ya kuma bayyana rashin bege game da ganin Nijeriyar da ya yi hasashe ga al’umma masu zuwa, inda ya danganta tafiyar siyasarsa zuwa ga ƙa’idoji maimakon son rai.

Da yake magana kan zaɓukan da suka gabata, Galadima ya bayyana yadda jam’iyyar NNPP ta yi galaba a kan ‘yan adawar ta duk da maguɗi da kuma munanan dabarun da aka yi musu.

Ya ce a shekarar 2011 da kuma a shekarar 2023, jam’iyyar NNPP ta shawo kan waɗannan ƙalubale don samun nasara.

Galadima ya soki yadda ɓangaren shari’a ke tafiyar da rigingimun zaɓe, inda ya bayyana wasu al’amura na nuna son kai da maguɗi.