Yadda aka shirya bikin bai wa Sarkin Kano sanda gobe Asabar

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Idan Allah ya kai mu gobe Asabar, 3 ga Yuli, 2021, a ke sa ran za a gudanar da babban taro na bai wa Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, sandar sarauta Sarkin Kano, wadda Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, zai yi.

Taron dai kamar yadda iyalan Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, kuma mahaifin sarkin na yanzu, suka sanar, wani muhimmin taro ne da aka shirya shi. Don haka ne ma aka fara hidimar bikin tun daga jiya Alhamis da shirya taro lakca, wanda haɗin gwiwa ne tsakanin Masarautar da Jami’ar Bayero. A taron dai, Farfesa Abdullah Uba Adamu ya gabatar da lakca mai taken Masarautar Kano jiya da yau da kuma gobe.

A rana ta biyu ta shagalin bikin kuwa, wato yau Juma’a, ana sa ran za a gudanar da zaman addu’a ne a Babban Masallacin Juma’a da ke Ƙofar Gidan Sarki ta ɓangaren Ƙofar Ƙwaru, sai kuma rana ta uku, wato gobe Asabar, za a yi taron bayar da sandar a filin wasa na Sani Abachi da ke Ƙofar Mata.

Taron dai kamar yadda iyalan Marigayi Sarkin Kano suka sanar, za a yi wani babban taro ne da zai ha]a mashahuran mutane daga kowanne ɓangare na Nijeriya da ma wasu sassa na duniya.

Babu mamaki kuma a ce rabon da a ga irin wannan taron tun lokacin Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, na raye, domin kuwa tsawon lokaci aka ɗauka ana shirin wannan bikin, wanda matakin farko da aka bi na shirin taron shi ne irin ziyarce-ziyarcen da Sarki Aminu Bayero ya rinƙa kai wa manyan fadojin sarakuna a dukkan fa]in ƙasar.

Shi dai Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama sarki ne a ranar 9 ga Maris, 2020, bayan da Gwamnatin Jihar Kano ta tuɓe rawanin Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sunusi II.

A ɗan lokacin da Mai Martaba Sarki Aminu Bayero ya yi a gadon mulki na shekara ɗaya da watanni ya naɗa manyan sarautu guda biyu. Ya naɗa Alhaji Sunusi Ado Bayero sarautar Wamban Kano, sai kuma Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba.