Yadda aka yi wa basarake da abokansa kisan gila a Ogun

Daga BASHIR ISAH

Al’ummar Agodo da ke yankin ƙaramar hukumar Ewekoro a jihar Ogun sun faɗa cikin yanayi na alhini da firgirci a ranar Litinin ɗin da ta gabata sakamakon kisan gilan da wasu da ba a kai ga sanin ko su wane ne ba suka yi wa sarkin yankin, Oba Ayinde Odetola.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, aika-aikar ta rutsa da wasu abokan sarkin su uku wanda aka ƙona su har lahira.

Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa kisan na da nasaba da rikicin sarautar Alagodo. An ce da ma tun farko akwai kwantacciya kan ko wane ne ya fi cancanta ya gaji kujerar sarautar yankin tsakanin jama’ar Ake da ta Owu na ƙasar Egba.

Wata majiya ta ce marigayin sarkin ɗan ɓangaren Ake ne daga Egba, sannna akwai batun cewa babu yadda za a yi ɗan Ake ya mulki garin da ‘yan Owu ne mafi rinjaye.

Bayanai sun nuna cewa ko a lokutan baya ba da daɗewa ba, an kashe wani ɗan’uwan sarkin a nan yankin.

Rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa an kashe Sarki Oba Odetola ne da misalin ƙarfe 11 na safe tare da wasu abokansa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a daren Litinin da ta gabata.

Inda ya ce, bayan da ɓatagarin suka yi nasarar raba sarkin da ransa, sai suka haɗa da shi da motarsa suka ƙona ƙurmus.

Ya ƙara da cewa, duk da dai kawo yanzu babu wanda aka kama da hannu cikin faruwar badaƙalar, amma cewa sashen binciken manyan laifuka na rundunarsu ya soma gudanar da bincike kan lamarin domin bankaɗo miyagun don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata.