Mutum 30 sun mutu, an ceto 719
Za a fuskanci ɓarkewar kwalara a Maiduguri, inji Majalisar ɗinkin Duniya
Tinubu ya lashi takobin kawo ƙarshen ambaliya a Nijeriya
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, da sanyin safiyar ranar Talata ta girgiza al’ummar Nijeriya, inda ta mamaye ɗaruruwan gidaje tare da lalata ɗimbin dukiya a jihar da uwa-uba asarar rayuka.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta ƙasa NEMA ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa muhallansu.
Hakazalika mutane 30 sun mutu a yayin da aka ceto wasu 719 da suka maƙale a saman rufin gine-gine bayan ambaliyar Kazalika mutanen da suka maƙale a wasu wurare da ruwa ya yanke su da sauran al’umma na tsawon kwanaki na neman a kawo musu ɗaukin gaggawa, a yayin da sojoji da sauran hukumomi ke ci gaba da aikin ceto.
Har yanzu dai iyalai na ci gaba ƙoƙarin gano ƙananan yara da ’yan uwansu da suka ɓace tun bayan tasowar ambaliyar da ta girgiza al’ummar Nijeriya da sauran wurare.
Mazauna garin, waɗanda akasarinsu ‘yan ƙaramar hukumar Jere ne, an tilasta musu barin gidajensu.
Ambaliyar ruwan dai ta biyo bayan rugujewar madatsar ruwa ta Alau, wadda daga kimanin kilomita 10 zuwa cikin babban birnin jihar.
Matsuguni da wuraren kasuwanci sun nutse cikin ruwa da suka haɗa da shahararriyar Kasuwar Monday da dubban gidaje da kadarori, kamar fadar Shehun Borno, Shehuri, Gwange, Adamkolo, Gamboru, Fori, Bulabulin, unguwannin gidan waya, Moromoro, da kwastam. Gadar da dai sauran su ma abin ya shafa.
Yawancin mazauna garin da suka zanta da Manhaja sun ce ba su iya gano ‘yan uwansu ba a halin yanzu.
Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Malam Barkindo Mohammed, ya bayyana cewar halin da ake ciki a Maiduguri sakamakon afkuwar ambaliyar ruwa ya munana.
Mohammed, ya ce hukumar ta fara aikin ceto da kuma raba buhunan yashi don hana ruwan ya ƙara kwarara zuwa wasu yankuna.
“Muna kan aikin ceto yanzu haka, kuma mun raba buhunan yashi a Gozari. Yayin da nake magana da ku yanzu, ni da ma’aikatana mun maƙale; mun zo ceton wasu mutane amma yanzu muna cikin tsaka mai wuya,” in ji shi.
Wasu mazauna garin na zaune ko kwance ne a ƙarƙashin bishiyoyi tare da iyalansu.
Wani magidanci mai mata biyu da yara shida, Musa Abbas, ya ce ba shi da inda zai je.
Ya ce ’yan uwansa suna zaune a yankin Bulumkutu, amma ya ce kafin zuwa wajensu dole ne a haye wata gada wadda ruwa ya shanye.
“Yanzu gadar ta nutse a cikin ruwa; ba zan iya hayewa ba sai dai ‘yan uwana su zo su ɗauke ni. A nan za mu kwana, kuma za mu ci gaba da addu’ar kada ruwan sama ya sake sauka,” in ji Abbas.
Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ce mutane miliyan guda ne ambaliyar ta shafa a jihar ranar Talata.
Gwamnan ya ce ambaliyar ta shafe kashi ɗaya bisa huɗun garin Maiduguri, inda ake fargabar ɓullar cututtuka masu yaɗuwa sakamakon cikar masai da juji da sauransu.
Da yake rabon kuɗaɗe da dafaffen abinci ga ’yan gudun hijirar da suka fake a Sansanin Gudun Hijira na Bukassi da ke Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatin tarayya ta ba wa Jihar Borno tallafin Naira biliyan uku domin waɗanda ambaliyar ta shafa, kuma za a yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar da ta dace.
Ya ce tuni aka riga aka kafa kwamitin bayar da agajin gaggawa na lafiya domin daƙiile annobar ambaliyar ruwa a Maiduguri da yankin Jere.
Hakazalika, tawagar bincike da aikin ceto ta fara aiki a wuraren da abin ya shafa domin tantance irin asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi.
“Kun ga yadda ruwa ya mamaye yankin gaba ɗaya, ƙazanta ta yaɗu, wanda hakan ne nufin za a kamu da cututtuka masu yaɗuwa, amma Insha Allahu za mu shawo kan lamarin.
“Zuwa yanzu dai ba mu iya tantance yawan asarar da aka yi ba, amma kusan kashi ɗaya bisa huɗu na garin Maiduguri ya cika da ruwa.
“Mutanen da abin ya shafa sun kai miliyan guda, abin da muke yi a safiyar yau shi ne ba su agajin gaggawa na abinci da sauran kayayyaki,” inji shi.
Da yake amsa tambaya kan musabbabin ambaliyar, gwamnan ya ce danganta shi da sauyin yanayi da ya haifar da mamakon ruwan sama da ake fama da shi a bana.
Ya ce ruwan ya ƙwace daga Madatsar Ruwan Alau, ya shigo Maiduguri, haɗi yawan ruwan da aka sako daga sauran madatsar ruwa a Kamaru.
Zulum ya ba da tabbacin cewa za a sake gina madatsar ruwan tare da ƙara karfinta, sannan za a rushe haramtattun gine-ginen da ke kan hanyoyin ruwa da wuraren da ake fama da ambaliya.
Ambaliyar wadda ita ce babbar ambaliya da aka taɓa yi a Jihar Borno, ta sa sabon gidan yarin da aka yi a Maiduguri ya fuskanci rugujewa sosai, lamarin da ya haifar da ruɗani yayin da fursunoni da dama suka yi amfani da damar wajen tserewa bayan da ruwa ya raunana ganuwar gidan yarin.
Yayin da bangon gidan yarin ke faɗi, fursunonin sun yi amfani da damar wajen guduwa, lamarin da ya sa jami’an tsaro da ke bakin aiki suka mayar da martani cikin gaggawa. A ƙoƙarin da ake na ganin an dawo da iko, jami’an tsaro sun fara harbi a iska a wani yunƙuri na tsoratar da waɗanda ke yunƙurin guduwa.
Har yanzu dai ana ƙoƙarin shawo kan al’amura yayin da hukumomi ke ƙoƙarin zaƙulo waɗanda suka tsere tare da dawo da zaman lafiya a gidan yarin.
Kazalika Gwamna Zulum, ya rufe ɗauƙacin makarantun firamare da sakandare nan take sakamakon ruwan sama da albaliya mai ƙarfi.
Zulum ya umarci ma’aikatar ilimi ta rufe makarantun na tsawon makonni biyu, domin guje wa asarar rayukan ɗalibai a sakamakon ambaliyar.
Wannan mataki na zuwa ne ranar Litinin da makarantu suka dawo daga hutun ƙarshen shekara domin fara zangon karatu na 2024/2025.
Kwamishinan Ilimin Jihar, Lawal Wakilbe ya shaida wa Manhaja cewa ana sa ran buɗe makarantun bayan makonnni, lokacin da ake fatan ambaliyar ta yi sauƙi.
Wakilbe ya ce ɗaukar matakin rufe makarantun ya zama dole ne bayan zaman kwamitin da gwamnatin Zulum ta kafa domin taƙaita asarar rayuka a sakamakon ambaliya a jihar.
Kwamishinan ya ce ambaliyar ta zama babban ibtila’i a jihar inda ta raba dubban mutane da muhallansu.
’Yan Kasuwar Monday Market da sauransu a Maiduguri sun tafka mummunar asara sakamakon ambaliya bayan fashewar Madatsar Ruwa ta Alau mai nisan kilomita 10 daga garin.
Wani ɗan kasuwa ya ce, “Duk shagunan da ke Monday Market da Post Office ruwa ya shanye su.”
Wakilinmu a garin Maiduguri ya zagaya garin, inda ya iske ’yan kasuwar Monday Market suna lissafin irin asarar da suka yi sakamkon ibtila’in.
Wasu daga cikinsu sun nuna matuƙar kaɗuwarsu da kuma tunanin yiyuwar maye gurbin abin da suka rasa a ambaliyar.
Wani mai sayar da sukari da fulawa a kasuwar, Muhammad Bulama, ya ce ambaliyar ta shanye kasuwar gaba ɗaya.
“Duk shagunanmu da ke kallon gidan Marigayi Alhaji Mai Sugar sun yi ambaliya, sukari da fulawa da shinkafa da kayan girki na miliyoyin Naira sun lalace.
“A sa mu a add’ua! Buhunan kayan abinci irin su sukari da shinkafa da gishiri da taliya da sauransu duk sun jiƙe sun narke,” in ji shi.
Hakazalika ambaliya ta mamaye Gidan Zoo na Kyarimi ta wuce da namun dajin da ke ciki, inda a halin da ake ciki namun dajin suke neman mafaka.
Wani mazaunin yankin ya ce, “yanzu haka mun fice daga unguwar saboda gudun hari daga namun daji da ƙwarin da ke gidan zoo.
Rundunar ’yan sanda a Jihar Borno ta buƙaci jama’a da su ƙaurace wa yankunan da aka samu ambaliya zuwa wasu wurare masu aminci.
A nata ɓangaren, Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙungiyoyin Al’umma (CSOs) ta ce ambaliyar da ke gudana a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya shafi aƙalla maƙabarta da wani gidan kula da dabbobin daji da kuma zagwanyewar wasu yankunan birnin.
ƙungiyar ta nuna damuwa musamman kan al’ummar dake rayuwa a yankunan da lamarin ya shafa.
Wannan shi ne ambaliya mafi muni cikin shekaru 30 da yankin ya fuskanta tun da aka yi makamancinsa a 1994 wanda hakan ya sa mutane da dama suka rasa matsugunansu.
Cikin saƙonni ta mabanbanta hanyoyi da CSOs suka fitar, sun ce lamarin ya yi ƙamari sosai.
Shugaban CSOs na yankin Tafkin-Chad, Ahmed Shehu ya ce, kawo yanzu ba a san halin da dabbobin da suka fice daga gidan kula da su na Sanda Kyamiri suke ba.
ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan al’amarin.
Kazalika, Shehu ya yi kira ga ƙungiyoyin al’umma su bada agajin gaggawa musamman na abinci, kayan sakawa da kayan abinci ga waɗanda abin ya shafa.
Majalisar ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi game da yiyuwar ɓarkewar cutar Kwalara a sansanonin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da aka kafa a Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon ambaliyar.
Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar ɗinkin Duniyar ya fitar, ya ce abubawan da za a buƙata cikin gaggawa sun haɗa da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa, inda ya ƙara da cewar wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurɓace, kuma na iya janyo ɓarkewar cututtuka irinsu Kwalara.
An ruwaito rahoton na cewa, “buƙatun gaggawa da ake da su sun haɗa da abinci da matsuguni da tsaftataccen ruwan sha, saboda wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurɓace.”
A wani hasashe kuma da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NIMET ta fitar, ta ce za a samu ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya a jihohi 12 mako mai zuwa.
Jihohin da ake sa ran samun ruwan saman sun haɗa da Bauchi, Neja, Bayelsa, Kaduna, Filato, Babban Birnin Tarayya (FCT), Taraba, Kuros Riba, Akwa-Ibom, Ribas da Delta.
Sannan rahoton ya nuna cewa akwai jihohi da za a samu ruwan saman amma matsakaici, jihohin sun haɗa da Adamawa, Katsina, Zamfara, Kebbi, Nasarawa, Kwara, Benue, Ebonyi, Imo, Anambara, Edo, Ondo, Ekiti, Osun, Oyo, Ogun da Legas.
Hukumar ta NIMET ta yi gargaɗin cewa ruwan saman ka iya haifar da ambaliya musamman a kan tituna da gadoji. Hukumar daga ƙarshe ta ja hankalin mutane da su guji shiga cikin ruwa mai gudana domin gudun faɗawa cikin haɗari.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana matuƙar damuwarsa game da ambaliyar ruwan da ta shafi wasu sassan Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar, musamman ga iyalan da suka rasa dukiyoyinsu, sakamakon iftala’in da ambaliyar ruwan ta haddasa.
A ɓangare guda kuma, hukumomin da abin ya shafa na ci gaba da tantance irin ɓarnar da ambaliyar ta yi, shugaban ya yi kira da a gaggauta kwashe mutanen daga yankunan da abin ya shafa.
Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Babagana Umara Zulum cewa Gwamnatin Tarayya a shirye ta ke ta ba da haɗin kai wajen samar da kayayykin buƙatun jin ƙai ga mutanen da abin ya shafa.
Ya kuma umurci Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa da ta gaggauta agazawa waɗanda ambaliyar ta shafa.
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ke bayyana hakan a yayin da ya yi saukar gaggawa a birnin Maiduguri inda ya kai ziyarar gani da ido kan ambaliyar da ta rutsa da dubban mutane a garin.
Mataimakin ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta sa ƙafar wando ɗaya da ƙalubalen ambaliyar ruwa a Nijeriya ta hanyar amfani da taswirar da za ta kawo maslaha ta dindindin.
Shettima, wanda ke jawabin cikin ƙaduwa a lokacin da yake tantance irin ɓarnar da ambaliyar ta yi a garin Maiduguri, ya jajanta wa waɗanda ibtila’in ya rutsa da su, inda ya bayyana musu cewa, shugaba Tinubu na tare da al’ummar da abin ya shafa, kuma gwamnatin tarayya za ta samar da dukkan abinda ake buƙata domin tabbatar da tsaro da tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa.
Shettima ya danganta ambaliyar da ɓallewar madatsar ruwa ta Alau wanda ya ta’azzara lamarin har ya zarce irin wanda aka taɓa samu a baya. Sai dai kuma ya jaddada aniyarsa ta samar da mafita mai ɗorewa.
Mataimakin ya kuma yi kira da a ci gaba da wayar da kan al’umma kan ƙaruwar barazanar da sauyin yanayi ke haifarwa tare da jaddada aniyar gwamnati ta magance waɗannan ƙalubalen gaba ɗaya.
