Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Femi Otedola, ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata ’yan Nijeriya, musamman gwamnati su goyi bayan shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, ta hanyar samar da yanayi mai kyau don ganin kasuwancinsa ya bunƙasa.
Ya bayar da hujjar cewa gudunmawar da Dangote ya bayar wanda ya wuce wuraren masana’antu zuwa muhimman ababen more rayuwa, dole ne a gane su kuma a tallafa masa ta kowace hanya.
Otedola, wanda ya tashi don kare abokinsa kuma abokin kasuwancinsa a wani rubutu a shafinsa na Ɗ a ranar Talata, ya bayyana Dangote a matsayin “Kyautar Allah ga bil’adama”.
“A Nijeriya muna da namu, kuma ya zama wajibi mu gane da kuma tallafa masa. Aliko Dangote ya karya kowace iyaka a harkokin kasuwanci da masana’antu na duniya. Gudunmawar da ya bayar ba wai kawai shaida ce ta haskakawarsa ba amma ginshiƙi ne ga cigaban al’umma.
“Tallafawa zakarun cikin gida irinsu Dangote yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa da kuma ’yancin cin gashin kai. Mu ci gaba da ƙarfafawa da tallafa wa waɗannan masu hangen nesa da ke kawo ci gaban ƙasarmu,” inji Otedola.
