‘Yan Nijeriya ba su da hujjar kukan yunwa, inji Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce, ‘yan Nijeriya ba su da wani dalili na yin kuka akan yunwa a lokacin da ƙasar ke da albarkacin katafarun filayen noma.

Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Tambari Hausa TV, wacce aka yaɗa a daren Laraba.

Yayin da ya ke amsa tambaya kan yadda ake fama da yunwa a ƙasar, shugaban ya ce, duk wanda da gaske yunwar ya ke ji, to kuwa zai ɗauki kayan noma ya nufi gona.

A cewarsa, rufe iyakokin ƙasa da sauran manufofin da gwamnatinsa ta ɓullo da su, don tabbatar da samar da abinci a ƙasat, ya haifar da sakamako mai kyau.

“Idan kuna ƙoƙarin ku kai rahotona ga ‘yan Nijeriya cewa, ban cika alƙawarina ba, bari na tambaye ku; lokacin da na hau mulki, ban bada umarnin rufe iyakokin ƙasa ba har kusan shekaru biyu?”

“Na ɗauki wannan matakin ne na dakatar da shigo da shinkafa daga ƙasashen waje, na ce mu noma abin da muke ci ko kuma mu mutu da yunwa.

“Na ce, tunda mu na da filin noma kuma Allah Ya albarkace mu da ruwan sama, wane dalili ne ɗan Nijeriya zai ce yana fama da yunwa? Idan ka na jin yunwa ka tafi gona,”inji Buhari.