Gargaɗin yiwuwar harin ta’addanci daga Amurka da Ingila

A ranar 23 ga Oktoba, 2022, Amurka da Birtaniya suka yi gargaɗi kan yiwuwar a kai harin ta’addanci a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, musamman kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da makarantu, da dai sauransu. Gwamnatin Birtaniya ɗin ta ƙara da cewa hare-haren na iya zama kan mai-uwa-da-wabi kuma zai iya shafar muradun ƙasashen yamma da ma wuraren da masu yawon buɗe ido ke ziyarta.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke yaƙar masu tayar da ƙayar baya da sunan addini a yankin Arewa maso gabas, amma a watan Yuli ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin wani samame a wani gidan yari da ke Abuja, wanda ya yi nasarar tserewar fursunoni kusan 879, lamarin da ya haifar da fargabar cewa ‘yan ta’adda masu tayar da ƙayar baya na kutsowa daga yankunansu.

Sakamakon barazanar, Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce, akwai ƙaruwar kasadar ta’addanci a Naoeriya, musamman Abuja, sannan ya ƙara da cewa manyan kantunan kasuwanci da cibiyoyin tabbatar da doka da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na daga cikin wuraren da ke fuskantar hadarin.

A makon jiya Talata, gwamnatin Amurka ta kuma ba da izinin ɗebo ma’aikatanta da iyalansu daga Nijeriya. Wasu kafafen yaɗa labarai sun yi ikirarin cewa abin da ya jawo sanarwar ta’addancin shi ne kame ɗaya daga cikin fursunonin gidan yarin Kuje da ya tsere daga gidan yari a ranar 5 ga Yuli, 2022 amma an sake kama shi a cikin harabar ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja.

A harin da aka kai gidan yarin Kuje, an ce fursunonin 879 sun tsere. Wadannan sun haɗa da ’yan ƙungiyar Boko Haram 68 da ake tsare da su a gidan yari.

Wannan ba shi ne karo na farko da aka fara ba da sanarwar wannan lamari ba. A watan Disambar 2017, Amurka da Birtaniya sun yi irin wannan gargaɗin, wanda ya sa Sufeto Janar Ibrahim Idris, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda a Babban Birnin Tarayya, Abuja, Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa da Yobe da su tabbatar da suna na sintiri na awa 24 a cibiyoyin ibada, makarantu, kasuwanni, wuraren shaƙatawa da tashoshin motoci. Har ila yau, a cikin watan Disamba na 2021, fadar shugaban ƙasar ta yi gargaɗi game da shirin kai hari da wasu ‘yan ta’adda daga Mali su ke niyyar yi a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Hatta hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu dalilin fitar da irin wannan faɗakarwa a baya. A cikin watan Yunin 2019, alal misali, hukumar ta DSS ta tayar da hankalin jama’a game da makircin da ake zargin wasu ’yan zagon qasa da masu rashin bin tafarkin demokuraɗiyya na haddasa rashin jituwa da tashin hankali a Nijeriya. Hukumar tsaro ta yi irin wannan ƙararraki a watan Yuli 2020 da Janairu 2021. Baya ga haka, Gwamna Abdulahi Sule na Jihar Nasarawa ya yi gargaɗi a watan Janairun 2021 game da ’yan Boko Haram da suka zauna a kan iyaka da Abuja.

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya kuma sanar da al’ummar ƙasar a shekarar da ta gabata kan kasancewar ’yan Boko Haram a jiharsa, inda ya yi gargaɗin cewa Abuja ma tana cikin haɗari.

Gargaɗin hari samfurori ne na tattara bayanan sirri. Babu wani ofishin jakadanci da zai tashi kawai ya ba da sanarwar idan babu dalilinsa. Abin da ya kamata kowace ƙasa mai ma’ana ta yi shi ne ta binciki bayanan da kuma shiryawa da kyau don tunkarar duk wani hari idan ya zo.

Don haka muna ƙalubalentar gwamnatin tarayya ta bakin ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed kan gargaɗin ta’addancin da aka yi kwanan nan. Ministan ba kwararre ne kan harkokin tsaro ba. Sai dai yadda ya yi watsi da rahoton ya sanya shakku kan shirin da Nijeriya ke da shi na tashi tsaye wajen ganin an daƙile ayyukan ta’addanci a ƙasar. Ya yi ikirarin cewa, ’yan Nijeriya sun fi zaman lafiya a yanzu fiye da da.

A bayyane ya ke wannan ba gaskiya bane. Har ila yau, Lai Mohammed ya yi ƙoƙari ya rage faɗakarwa ta hanyar jawo hankali ga harbe-harbe da sauran kashe-kashen rashin hankali a Amurka.

“Yanzu sun fara hasashen gaibu ne? Wace makaranta ce za a hara a gaba? Shin ’yan Nijeriya da ke Amurka suma suna cikin ƙoshin lafiya ne?” Ya tambaya.

Batun tsaro ba batun farfaganda ba ne. Mun yi imanin Amurka tana da hanyar sadarwa ta sirri da ta dace don tafiyar da wasu lamuran tsaro. A shekarar 2020, ta kuɓutar da ɗan ƙasarta, Philip Watson, da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a Nijeriya.

Sojojin Amurka na musamman (Navy Seal) sun kai farmaki a kogon masu garkuwa da mutane, inda suka kashe shida daga cikinsu tare da kuvutar da Watson. An ruwaito zaya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya tsere.

Haka rundunar sojojin ruwa ta kashe shugaban al-Qaida, Osama bin Laden a gidansa da ke Pakistan a shekarar 2011. Ministan ya kuma yi ikirarin cewa jami’an tsaronmu sun yi taka-tsantsan. Tambayoyin su ne: Shin sun taka rawar gani lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari gidan yarin Kuje a watan Yulin bana?

Ko sun kasance cikin shiri ne lokacin da ’yan ta’adda suka kai hari ga rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka kashe manyan jami’ai uku?

Da sauqi da rundunar ‘yan sanda suna yin abin da ake buƙata daga gare su. Jami’in hulza da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce rundunar za ta sake duba shawarwarin tsaro, ya kuma yi alƙawarin cewa ’yan sanda ba za su ɗauki duk wani bayanan sirri na barazana da za a yi ba.

Hedikwatar rundunar ta ce, Sufeto Janar na ’yan sanda, Usman Baba, ya umarci dukkanin kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da suka haɗa da na Babban Birnin Tarayya Abuja da su sake tsara tsarin gudanar da harkokin tsaro a yankunansu. Rahotanni sun ce Alkali Baba ya kuma sanar da wani atisaye na yaƙar ta’addanci, mai taken ‘Operation Darkin Gaggawa,’ wanda zai gudana a Abuja.

Muna sa ran maimakon yin watsi da irin wannan sanarwar, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta tilasta wa jami’an tsaro haɗin kai, musamman kan tattara bayanan sirri, kuma su kasance cikin shiri.

Sanin tsaro shine hanyar da za a bi kuma duk wani bayani game da tsaro yakamata a ɗauki shi da muhimmanci. Bai kamata a yi watsi da gargaɗin harin ta’addancin kwanan nan ba.